Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya da Amurka sun shiga wani ‘sabon babi mai kyau’ a dangantakarsu, biyo bayan tattaunawa mai zurfi da shugaban Amurka Donald Trump, wadda ta mayar da hankali kan tsaro, kasuwanci, da zaman lafiyar yankin.
Da yake magana da manema labarai a jirginsa na dawowa daga Azerbaijan a ranar Laraba, Erdogan ya ce ziyarar da ya kai Amurka a baya-bayan nan da kuma wayar da ya yi da Trump sun samar da "alamomi masu ƙarfafa gwiwa" kan muhimman batutuwan da suka yi tsami tsakanin ƙasashen biyu a 'yan shekarun nan.
"Mun tattauna kan F-35 da kuma takunkumin CAATSA, kuma mun sami sakonni masu ma'ana daga Shugaba Trump," in ji Erdogan.
"Turkiyya abokiyar aiki da ke biyan kuɗi ce a aikin samar da F-35. Cire mu daga shirin bai dace ba, kuma muna aiki don magance wannan," in ji shi.
Erdogan ya ƙara da cewa, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu kan aikin jirgin yaƙin da kuma sassauta takunkumin.
"Muna fatan waɗannan matakai za su ƙarƙare da kyau," in ji shi. "Ziyararmu ta samar da wani sabon babi a dangantakar Turkiyya da Amurka - wanda ke ƙarfafa abokantaka da tattaunawa."
Batun Halkbank “ba matsala ba ce”
Shugaban ya kuma ce, an warware matsalar da aka daɗe ana ta ce-ce-ku-ce a kan batun Halkbank, wadda ta yi tsami tsakanin Ankara da Washington.
"Shugaba Trump ya faɗa min kai tsaye, a lokacin ganawarmu da kuma a wayarmu ta ƙarshe, cewa, matsalar Halkbank ta ƙare," in ji Erdogan. "Wannan magana muhimmiyar magana ce ta siyasa."
Yayin da wasu matakai suka rage, Erdogan ya ce yana sa ran nan ba da jima wa ba za a rufe batun a hukumance.
"Muna son kammala wannan tsari cikin sauri da kyawu," in ji shi.
Rawar Turkiyya kan tsagaita wuta a Gaza
Erdogan ya kuma taɓo batun rikice-rikicen yanki, ciki har da halin da ake ciki a Gaza da Siriya, yana mai cewa tsarin diflomasiyya da tsaro na Turkiyya na ci gaba "a mataki mai girma."
Ya ce Ankara na ci gaba da tuntuɓar Amurka, Masar, da Hamas kan tsagaita wuta ta dindindin a Gaza kuma babban jami'in leken asirin Turkiyya na shiga tattaunawar da ake yi a Sharm el-Sheikh.
"Turkiyya na goyon bayan duk wani kokarin samar da zaman lafiya na gaskiya," in ji Erdogan, yayin da yake gargadin Isra'ila game da lalata tattaunawar. "Babban fifikonmu shi ne a samar da cikakkiyar tsagaita wuta mai ɗorewa, agajin jin kai mara fuskantar cikas, da sake gina Gaza ga Falasɗinawa."
Dangane da kasar Siriya, Erdogan ya jaddada cewa, Turkiyya ba za ta amince da sake haifar da tashin hankali daga 'yan ta'addar SDF ba, waɗanda haramtacciyar kungiyar PKK/YPG ke mamayewa, ko wata tsokana daga kasashen waje.
"Kada a kalli hakurinmu a matsayin rauni," in ji shi. "Ba za mu taba yarda a yi barazana ga 'yan gudun hijirar Siriya ba, wadanda ke da alaka da Ankara da Damascus za su yi nasara."
“Turkiyya na girma a matsayin mai karfi a yanki”
Da ya juya kan ziyarar da ya kai Azarbaijan, Erdogan ya ce shugabancin Turkiyya a cikin ƙungiyar kasashe masu magana da yaren Turkanci (OTS) a yanzu ya wuce hadin kan al'adu.
"OTS yanzu ba ƙungiyar al'adu ba ce kawai, ta zama wani dandamali don haɗin kai tare da samar da dabarun aiki," in ji shi. "Daga leken asirin zuwa tsaron kan iyakoki da tsaron yanar gizo, haɗin gwiwarmu yana zurfafa sosai."
Ya ce an sake nuna tasirin Turkiyya a duniya ta hanyar aikin Sumud Flotilla, inda ƙoƙarin Turkiyya ya tabbatar da sakin ɗimbin masu fafutuka da Isra'ila ke tsare da su.
"Wannan ya nuna irin ƙarfin da Turkiyya ke da shi na gaggawar ayyukan jin ƙai da diflomasiyya," in ji Erdogan. "Mun rubuta duk wani cin zarafi, kuma za mu bi kadin ganin an tabbatar da adalci ta hanyar diflomasiyya da doka."