Fiye da iyalai 21,000 a Sudan ne ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ya jawo ta shafa a jihohi 11 na kasar tun watan Yuni, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Sudan ta fitar ta ce jihohin Al-Jazirah da Al Qadarif sun fuskanci ambaliyar ruwa a wannan makon, wadda ta shafi iyalai 3,639 (mutane 18,195).
Wannan ya sa adadin iyalai da abin ya shafa ya kai 21,811 (mutane 113,723) a tsakanin 30 ga watan Yuni zuwa 14 ga Satumba, a cewar sanarwar.
Ta kara da cewa lamarin ya shafi jihohi 11 daga cikin 18 na kasar Sudan da suka haɗa da: Al Qadarif, Kassala da Red Sea (gabas); Arewa da Kogin Nilu (arewa); Sennar da Blue Nile (kudu maso gabas); Kordofan ta Yamma da ta Arewa (tsakiyar yamma); Darfur ta Tsakiya (yamma); da Al-Jazirah (gabas-ta tsakiya).
Lokacin damina
Sudan takan fuskanci ruwan sama mai yawa a lokacin damina, wanda ke gudana daga watan Yuni zuwa Oktoba, kuma yakan haifar da ambaliyar ruwa a kowace shekara.
Wadannan bala'o'i na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Sudan ke fama da yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojoji da dakarun sa kai na gaggawa (RSF), wanda ake ci gaba da yi tun tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023.
Rikicin dai ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 20,000, yayin da wasu kimanin miliyan 15 suka rasa muhallansu suka kuma zama 'yan gudun hijira, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin kasar, yayin da wani bincike da jami'o'in Amurka suka gudanar ya kiyasta adadin wadanda suka mutu ya kai 130,000.