AFIRKA
2 minti karatu
Wani awarwaron zinare mai shekaru 3,000 ya ‘ɓata’ a gidan adana kayan tarihi na Masar
Mahukuntan Masar ba su fayyace yaushe ne aka ga awarwaron a karo na karshe, amma sun ce awarwaron tun na zamanin Amenemope, fir’aunan Daula ta 21 da ta yi mulki a tsakanin 1070-945.
Wani awarwaron zinare mai shekaru 3,000 ya ‘ɓata’ a gidan adana kayan tarihi na Masar
Hukumar Kula da Kayan Tarihi ta Masa ta sanar da za a fara nuna 'Kayan Fir'aunoni" a Gidan Adana Kayan Tarihi na Masar. / Reuters
18 Satumba 2025

Ma'aikatar Kula da Kayan Tarihi ta Masar ta sanar da batan wani awarwaro na zinare mai shekaru 3,000 a dakin gwaje-gwajen maido da kayan tarihi da ke Alkahira.

Awarwaron da aka kwatanta a matsayin na zinare da aka ƙawata da "duwatsun lapis lazuli", mallakin zamanin Amenemope, Fir'auna na Daular Masar ta 21st (1070-945 BC).

A cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar a yammacin ranar Talata, ba ta bayyana lokacin da aka ga awarwaron a karo na karshe ba.

Kafafan yada labaran Masar sun ce an gano batan awarwaron a 'yan kwanakin nan yayin da ake gudanar da bincike kan kayayyaki, ko da yake ba a iya tabbatar da hakan ba.

Ma'aikatar ta ce an fara gudanar da bincike na cikin gida, kuma an sanar da cibiyoyin kula da kayan tarihi a dukkan filayen tashin jiragen sama na Masar, tashoshin jiragen ruwa da mashigar kan iyakokin kasar baki daya.

Ta kara da cewa, ba a sanar da lamarin nan take ba domin a ci gaba da gudanar da bincike, kuma ana ci gaba da gudanar da cikakkiyar kididdigar abubuwan da ke cikin dakin gwaje-gwajen.

Taskokin masarauta

Gidan adana kayan tarihi na Masar da ke dandalin Tahrir yana dauke da kayan tarihi sama da 170,000, gami da sassaken zinare na fuskar Sarki Amenemope.

Bacewar na zuwa ne makonni kadan kafin ranar 1 ga Nuwamba da aka shirya kaddamar da babban gidan adana kayan tarihi na Masar da aka dade ana jira.

Daya daga cikin fitattun kayan tarihi da ke gidan adana kayan tarihin, su ne taskokin kabarin sarki Tutankhamun, ana shirin dauke shi gabanin bude taron, wanda aka sanya shi a matsayin wani babban abu na al'adu a karkashin gwamnatin shugaba Abdel Fattah al-Sisi.

A 2021, Masar ta gudanar da babban faretin sauya wurin gawarwakin sarakuna da aka busar su 22, ciki har da na Ramses II da Sarauniya Hatshepsut, zuwa Gidan Tarihi na Wayewar Masarautar Masar a Tsohon birnin Alkahira, wani bangare na babban yunƙurin haɓaka kayan tarihi na Masarautar da jan hankula ga yawon buɗe ido.