AFIRKA
3 minti karatu
Harin RSF a wani masallaci da ke Darfur ya kashe mutum 75
Harin da dakarun RSF na Sudan suka kai na zuwa ne a daidai lokacin da suke ƙoƙarin korar sojojin ƙasar daga babban birnin yankin Darfur wato Al Fasher.
Harin RSF a wani masallaci da ke Darfur ya kashe mutum 75
A gefe guda kuma, hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa RSF na samun ci gaba a cikin Al Fasher da aka yi wa ƙawanya. / AP
21 awanni baya

Dakarun RSF na Sudan sun kashe mutum 75 a wani hari da jirgin sama mara matuƙi ya kai kan wani masallaci a sansanin 'yan gudun hijira a Darfur, kamar yadda wata kungiya mai bayar da agaji da ke aiki a wurin ta bayyana.

Harin ya faru ne a ranar Jumma’a a yayin da dakarun Rapid Support Forces (RSF) ke kokarin korar sojojin gwamnati daga babban birnin yankin Darfur, Al Fasher.

A cewar kungiyar Emergency Response Room da ke sansanin Abu Shouk, wani jirgi maras matuƙi ya kai hari kan wani masallaci.

"An ciro gawawwakin daga cikin baraguzan masallacin," in ji kungiyar a cikin wata sanarwa.

A gefe guda kuma, hotunan tauraron ɗan’adam sun nuna cewa RSF na samun ci gaba a cikin Al Fasher da aka yi wa ƙawanya.

Tsawon kusan watanni 18, RSF ta yi wa Al Fasher ƙawanya, inda ta riga ta karbe wasu sassan babban birnin jihar Arewacin Darfur.

Sojojin Sudan - wadanda sansanoninsu ke a Al Fasher sun fi mayar da hankali a yammacin birnin - yaƙin ya rutsa da su a a can tun Afrilun 2023.

Hotunan tauraron ɗan adam da Jami'ar Yale ta bincika ta hanyar Humanitarian Research Lab sun nuna cewa dakarun RSF suna samun ci gaba a wurare masu muhimmanci, ciki har da tsohon sansanin UNAMID - wata cibiyar da aka karfafa a yammacin Al Fasher da aka taba amfani da ita a matsayin hedkwatar haɗin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka, yanzu kuma tana zama hedkwatar abokan sojojin gwamnati, wato Joint Forces.

"RSF mai yiwuwa ta karbe tsohon sansanin UNAMID, hedkwatar Joint Forces," in ji Jami'ar Yale, tana nuni da barnar da aka gani a hotunan tauraron dan adam da aka tattara tsakanin Litinin da Alhamis.

Wani jami’in RSF, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin magana da manema labarai ba, ya ce: "Kusan karfe 2:00 na rana (Alhamis), dakarunmu sun karbe cikakken iko da sansanin UNAMID."

Mayakan RSF sun kuma karbe mafi yawan sansanin 'yan gudun hijira na Abu Shouk da yunwa ta addaba, wanda ke da yawan jama'a sosai, kimanin kilomita uku arewa da UNAMID, a cewar shaidu.

Wannan ya sanya filin jirgin saman Al Fasher - wanda ke zama hedkwatar sojojin gwamnati da ke kusan kilomita uku kudu da UNAMID - da kuma hedkwatar Runduna ta 6 ta sojojin gwamnati, kilomita biyar gabas da sansanin, waɗanda duka wurare ne da idan RSF ta yi harbi zai iya kaiwa.