Me zai faru ga takunkuman da Amurka ta sanya wa Venezuela bayan ta ɗauke Maduro
DUNIYA
4 minti karatu
Me zai faru ga takunkuman da Amurka ta sanya wa Venezuela bayan ta ɗauke MaduroBayan sace Maduro da kuma alƙawarin Washington na cin gajiyar man Venezuela, makomar takunkumin Amurka za ta yi muni. Amma shin 'yan Venezuela za su ga sassaucin tattalin arziki, ko kuma kamfanonin Amurka za su zama manyan masu cin gajiyar hakan?
Me zai faru ga takunkuman da Amurka ta sanya wa Venezuela bayan ta ɗauke Maduro / Reuters
5 Janairu 2026

A yanzy batun me zai faru da takunkuman da Amurka ta sanya wa Venezuela sun mamaye tattaunawar duniya bayan da sojojin Amurka suka ɗauke Shugaba Nicolas Maduro.

Sanarwar da Washington ta fitar kafin ta ɗauke Maduro a wani lamari mai ban mamaki a ranar Asabar, ta haɗa da hana jiragen ruwan dakon mai na Venezuela wucewa tare da kira ga kamfanonin Amurka da su zuba jari a fannin mai na Venezuelan, lamarin da ya nuna alamar samun sauyi a tsarin takunkuman.

Sai dai, babu tabbas kan ko waɗannan matakai za su samar da wani sauƙi ga al’ummar Venezuela ko kuma Amurka ce kawai za ta amfana bisa muradunta na samun mai.

Takunkuman sun mayar da hankali ne kan arziki fetur

Tsawon shekaru, takunkuman da Amurka ta kakaba wa Venezuela sun gurgunta fitar da mai, wanda a da shi ne ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar ta Kudancin Amurka.

Takunkuman da ke ci gaba da aiki, waɗanda aka ƙarfafa a ƙarƙashin gwamnatin Trump, sun toshe yawancin jigilar mai kuma da kai hari kan jiragen ruwa da ke jigilar man fetur na Venezuela, lamarin da ya dakatar da fitar da mai yadda ya kamata.

Wannan lamari ya sanya samar da mai a Venezuela yin ƙasa da ba a taɓa gani ba a tarihi da kuma tabarbarewar harkokin kuɗi na gwamnati.

Lasisin Chevron ne kawai ya ba da damar ci gaba da fitar da mai, amma tsarin takunkumai masu yawa sun ci gaba da aiki.

Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta kama Maduro da sha'awar da Amurka ta daɗe tana da ita ga man fetur na Venezuela, yana mai tabbatar da cewa kamfanonin Amurka za su sake gina kayayyakin samar da makamashi da suka lalace a ƙasar tare da dawo da samar da kayayyaki, wanda hakan zai laƙume biliyoyin kuɗi a wannan tsari.

Amma ƙwararru sun yi gargaɗin cewa rashin kwanciyar hankali na siyasa da lalacewar kayayyakin more rayuwa na nufin duk wata murmurewa za ta ɗauki shekaru da kuma neman zuba babban jari, ba wai kawai wani alheri ga rayuwar yau da kullum ta 'yan Venezuela ba.

Tsarin takunkuman Amurka shi ne jigo da ke tantance samar da mai na Venezuela. Masu sharhi daga kamfanonin hada-hadar kudade kamae su Goldman Sachs sun fahimci cewa samar da mai ka iya yin ƙasa a nan kusa, ya danganta da sassauta takunkuman da Washington ta yi da kuma yadda masu zuba jari suka mayar da martani don kare barazanar shari’a.

Wannan na nuna cewa ko da an ɗage takunkuman, to tasirin da Venezuela za ta ji nan da nan ka iya taƙaituwa.

Ɗage takunkumi?

Washington za ta iya sassauta takunkumin fitar da mai a madadin hukumomin riƙon ƙwarya na Venezuela ko kuma gwamnatin da za ta zo.

Irin wannan matakin zai iya jawo hankalin masu zuba jari na ƙasashen waje da fasaha, yana ƙara yawan samarwa da kuma samar da kuɗaɗen shiga na gwamnati wanda za a iya amfani da shi don magance ƙarancin abinci, magunguna da ayyukan yau da kullun.

Duk da haka, ɗage takunkumin nan take da alama ba zai yiwu ba tare da kwanciyar hankali na siyasa da kwangiloli masu aiki ba, domin kamfanonin mai na Amurka da yawa, wadanda ke da sha'awar albarkatun mai na Venezuela, suna cikin taka tsantsan a yayin da ake ci gaba da samun rashin tabbas na siyasa.

Matsalolin shari'a game da mallakar kadarorin man fetur na Venezuela da kuma bin dokokin kasa da kasa sun ƙara dagula lamarin.

Abin da zai iya faruwa daga ƙarshe

Wani abu da ake ganin shi ne sakamakon mafi yuwuwa shi ne sassauta takunkumin da aka danganta da takamaiman ma'auni, kamar sake fasalin ɓangaren mai ko ƙirƙirar tsarin siyasa na riƙon ƙwarya.

Masu goyon bayan sun ce wannan hanyar za ta iya daidaita muradun Amurka da farfadowar Venezuela, duk da cewa za ta samar da sakamako mai jinkiri da rashin daidaito ga 'yan ƙasar da ke fama da wahalhalun yau da kullun.

Yayin da Washington ke la'akari da matakan da za ta ɗauka na gaba, makomar takunkumin da Amurka za ta tsara yadda za a sake gina fannin mai na Venezuela da kuma waɗanda za su amfana daga wannan tsari.

Ga yawancin 'yan ƙasar Venezuela da ke fuskantar matsin tattalin arziki mai ɗorewa, duk wani sauyi a manufofi ba za a yi shi ne da alƙawarin saka hannun jari ba, amma ta hanyar ko zai samar da ci gaba a rayuwa ta yau da kullum.