Mai Shari’a Emmanuel Subilim na kotun masana’antu ta ƙasa da ke babban birnin Nijeriya Abuja, ya hana ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN) aiwatar da yajin aikinta kan Matatar Man Dangote.
Da yake yanke hukunci kan ƙarar da Matatar Dangote ta kai kotun, Mai shari’a ya hana waɗanda aka kai ƙarar, ciki har da kamfanin man Nijeriya NNPCL da hukumomi masu kula da haƙowa da dako da kuma sarrafa ɗanyen mai da iskar gas datse wa Matatar Dangote damar samun ɗanyen mai da iskar gas.
Wani babban lauya a Nijeriya, George Ibrahim, ne ya gabatar da ƙarar tare da gamsar da alƙalin da ya ba da umarnin.
Ƙungiyar PENGASSAN ce ta bayar da umarni ga ma’aikatanta da su katse duk wata hanya da matatar Dangote take samun ɗanyen fetur da iskar gas sakamakon rikicin da ya kaure a tsakaninsu bisa zargin korar ma’aikatanta da ke aiki a matatar da kuma batun zaɓin zama ‘ya’yan ƙungiyar.
Sai dai a matatar mai ta Dangote ta garzaya kotu domin hana aiwatar da matakin.
A hukuncinsa, Mai shari’a Subilim ya ce masu shigar da ƙarar sun yi daidai domin yajin aikin ma’aikatan PENGASSAN zai yi illa ga harkokin kamfanin tare da katse samar da muhimmin abu (man fetur) ga ‘yan Nijeriya.
Alƙalin ya ce abin da ya dace da adalci shi ne kotun ta hana waɗanda aka kai ƙarar domin tabbatar da zaman lafiya a ma’aikatar da kuma ƙara taimakawa wajen ci gaba da yi wa ‘yan Nijeriya muhimmiyar hidima har zuwa lokacin da za a ji asalin ƙarar.
Yayin da yake ba da umarnin hana waɗanda aka kai ƙarar ɗaukar mataki, Mai shari’a Subilim, ya bayar da umarnin cewa a kai wa waɗanda aka kai ƙarar umarnin dakatar da ɗaukar matakin nan-take.
Ƙoƙarin sansatawa ya ci tura
Zaman da gwamnatin Nijeriya ta shirya domin yin sulhu tsakanin Matatar Dangote da ƙungiyar PENGASSAN ya kasa cim ma matsaya ranar Litin da daddare.
Zama da Ministan Ƙwadago da ayyukan yi, Muhammad Dingyadi , ya jagoranta ya haɗa masu ruwa da tsaki ciki har da shugabannin ƙungiyar PENGASSAN da wakilan Matatar Dangote da Ministan Kuɗi da daraktoci daga hukumomin NUPRC da NMDPRA.
Rahotanni dai sun ce zaman da aka yi a Abuja an fara shi ne da misalin ƙarfe 3:50 na rana maimakon ƙarfe 2: 00 da aka tsara, kuma ba gama shi ba sai bayan ƙarfe 12:00 na dare inda aka tashi ba tare da cim ma matsaya ba.
Sai dai kuma rahotanni sun ce ana ganin za a ci gaba da tattaunawar ranar Talata da misalin ƙarfe 2:00 na rana.