Gwamnoni da shugabanni daga yankin arewacin Nijeriya sun jaddada mahimmancin yankin ya kasance tsintsiya maɗaurinki guda don ta haka ne kawai za a magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki da suka addabi yankin tsawon shekaru.
Shugabanni da sauran manyan jagorori na arewacin ƙasar sun bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin wani babban taro kan yankin wanda ya mayar da hankali kan zuba jari da bunƙasa masana’antu na 2025 (NNIIS).
Taken taron, wanda Kungiyar Dattawan Arewa Northern Elders Forum (NEF) ta kira, shi ne gano hanyoyin bunƙasa haƙar ma’adanai da aikin gona da kuma lantarki wato ’Unlocking Northern Nigeria’s Mining, Agricultural and Power Potentials (MAP2035)’.
Kungiyar NEF ta ce MAP2035 wani shiri ne na musamman wanda za a bi daki-daki tsawon shekara 10 da niyyar kawo sauyi a yankin kuma yankin ya zama cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da masana’antu da kuma ci-gaba.
Tsawon shekaru yankin yana fama da matsalolin ’yan bindiga da rikicin Boko Haram da rikicin makiyaya da manoma da kuma matsalar satar mutane don neman kuɗin fansa.
Yayin da suke jawabi a lokacin taron, gwamnonin jihohin Zamfara da Nasarawa da kuma Gombe sun bayyana cewa ya kasancewar kawunan jihohin arewa a rabe, ya rage ƙarfin tasirin yankin kuma hakan yana ci gaba da mayar da yankin baya.
Gwamnonin sun buƙaci yankin ya dunƙule waje guda don ta haka ne zai iya magance matsalar tsaro kuma ya samar da hanyoyin da za su kawo haɓakar tattalin arziki.
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ce tsaro shi ne mahimmin ginshiƙin da ke kawo ci-gaba. Ya ce masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasar ba za su zuba kuɗinsu a wurin da babu tsaro ba.
Sannan gwamnan ya buƙaci jihohi 19 na yankin su haɗa ƙarfi waje guda musamman ta fuskar musayar bayanan sirri da sauran matakan tsaro da jihohin suke ɗauka.
A nasa ɓangaren Gwamnan Jihar Nasarawa ya ce jihohin yankin suna da ɗimbin hanyoyin samun kuɗin shiga, inda kuma ya shawarci gwamnoni da su riƙa amfani da kudaden da jihohinsu ke samu wajen bunƙasa jihohin.
Sannan gwamnan ya ce jiharsa ta sake fasalin yadda ake haƙo ma’adanai da aikin gona wanda ya ce hakan zai taimaka wajen bunƙasar jihar da kuma yankin baki ɗaya.
Shi ma Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ya ce ƙarancin abubuwan more rayuwa da ake da shi a yankin yana cikin dalilan da suka jawo cikas ga tattalin arzikinsa.
Ya ce Allah Ya albarci yankin da ma’adanai da ƙasa mai albarka da yawan jama’a amma kuma idan babu titin jirgin ƙasa da lantarki da tsarin ajiye amfanin gona, to ba za a ci cikakkiyar gajiyar arzikin ba.