Ma’aikatar tsaron cikin gida ta ƙasar Ghana za ta ƙaddamar da lasisin bindiga na intanet daga watan Disambar shekarar 2025 domin inganta sa ido kan mallakar bindiga da kuma rage mallakar bindiga ba bisa ƙ’ida ba a ƙasar.
Ministan tsaron cikin gida na Ghana, Muntaka Mohammed Mubarak ne ya shaida wa kwamitin binciken kuɗi a majalisar dokokin ƙasar cewa wata kafa ta intanet ce za ta maye gurbin tsarin takarda da ake amfani a halin yanzu domin inganta sabunta lasisi.
Ya ce sabon tsarin zai bai wa masu lasisi damar sabunta lasisinsu ta intanet kuma su biya kuɗi ta wayar salula.
Kazalika ya ce tsarin zai tura wa mutane saƙon tuni watanni uku gabanin ƙarewar lasisinsu tare da hana waɗanda ke da tarihin aikata laifi sabunta lasisinsu.
"Za a haɗa dukkan lasisin bindiga da katin [shaidar ɗan ƙasa] na Ghana domin sauƙaƙa bibiyar waɗanda suka mallaki bindigogi lamarin da zai rage yawan aikata laifuka a ƙasar, in ji ministan tsaron cikin gida.
Bayanin ministan ya biyo bayan ƙorafin da wata mambar kwamitia, Mis Helen Adjoa Ntoso, ta nuna ne inda ta ce bindigogi 606 ne a hannun fararen-hula ba bisa ƙa’ida ba saboda masu bindigogin ba su sabunta lasisinsu ba.
Babban Sufeto Janar na ’yan sandan ƙasar, Mista Christian Tetteh Yohuno, ya ce rundunar ‘yan sandan ƙasar ta tara bayanan duk masu lasisi a komfuta kuma tana wayar da kansu domin su sabunta lasisinsu kan lokaci.
Ya bayyana cewa lasisi na kai wa shekara ɗaya ne, amma da yawa daga cikin masu riƙe da su ba sa sabunta su har sai lokacin da matsala ta auku.
Mubarak ya ce tsarin komfuta zai inganta sa ido kan lasisin da suka ƙare da kuma ƙarfafa ikon ‘yan sanda wajen ƙwace makaman da ake riƙe da su ba bisa ƙa’ida ba.