Kamar yadda aka saba a watan Satumban kowace shekara, Birnin New York na Amurka yakan karɓi baƙucin babban taron diflomasiyya na duniya, inda yake cika ya batse.
Akan ga shingayen binciken kan hanyoyi a sassan birnin, jami’an tsaro kan mamaye tituna, ƙarar jiniya ta karaɗe garin, duk ba don komai ba sai saboda Taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya da ake kira da UNGA.
Bari mu yi nazari kan manyan abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a taron UNGA na 2025 kuma karo na 80, wanda aka shafe mako guda ana yi.
Da ma dai taron UNGA wani babban dandalin ne na luguden laɓɓa, inda shagabannin duniya ke nuna wa juna yatsa, ko kuma a ce, sukan je su zazzage duk wata ƙullalliyar gaba da suke yi wa junansu.
Tarihi cike yake da shugabannin ƙasashen da suka gabatar da jawabin huce haushi, inda ake yawan tunawa da tsofaffin shugabanni irin su marigayi Mu’ammar Gaddafi na Libya, da Robert Mugabe na Zimbabwe, da Fidel Castro na Cuba, da Yasser Arafat na Falasɗinu, da Mahmoud Ahmedinejad na Iran, waɗanda suka yi ƙaurin suna wajen ragargaza da bankaɗe-bankaɗe kan zaluncin duniya.
A bana ma ba ta sauya zani ba, sai dai ma a ce kamar wannan karon shugabannin da suka je taron da fushi da tankiya a ransu, sun fi na ko yaushe yawa.
Babban batun da ya mamaye taron UNGA na wannan shekarar shi ne na yaƙin Gaza, inda kusan duka ƙasashen sai da suka taɓo shi.
Alal misali, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yi zazzafan jawabi, inda ya zargi Isra'ila da aikata kisan ƙare-dangi a Gaza. Erdogan ya dinga ɗaga hotunan da ke nuna mummunan halin da Falasɗinawa ke ciki a Gaza, kuma ya yi kira ga al'ummar duniya da su ɗauki mataki cikin gaggawa don kawo ƙarshen zubar da jinin da aka shafe fiye da kwanaki 700 ana yi.
Sauran shugabannin da suka caccaki Isra’ila da nuna mata yatsa a UNGA sun haɗa da Nijeriya, da Ghana, da Kenya, da Columbia, da Chile, da Indonesia, da Saudiyya, da Qatar, da Jordan, da Faransa, kai har ma da Sarkin Spain da ma wasu da dama.
Baya ga yin tir da ta’addancin Isra’ila, masu jawabin sun jaddada neman a tabbatar da samar da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin-kanta, da gurfanar da Netanyahu a gaban Kotun masu aikata miyagun laifuka ta duniya, ICJ.
Akwai kuma Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian wanda ya nuna wani littafi da ke ɗauke da sunaye da hotunan 'yan ƙasarsa da kuma Falasɗinawa fararen-hula da Isra'ila ta kashe, yana mai cewa dole a yi maganin Isra’ila.
Sai Shugaban Syria, Ahmed Al Sharaa, wanda duk da cewa wannan ce bayyanarsa ta farko a gaban taron UNGA, kuma shi ne shugaban Syria na farko da ya halarci taron na MDD tun shekarar 1967, shi ma sai da ya amaye abin da ya ƙunso a cikinsa, wanda mafi yawa a kan ayyukan Isra’ila ne a yankin Gabas ta Tsakiya, da barazanar haifar da sabon rikici a yankin.
Wani abin lura da UNGA na bana shi ne, duk da wannan gagarumin taro na shugabannin ƙasashe da jami’an diflomasiyyar duniya, Amurka ta hana Shugaban Kasar Falasɗinu, Mahmood Abbas halartar zauren, bayan hana shi biza, duk da cewa rabin batutuwan taron a kan ƙasarsa ne.
A ƙarshe dai sai ta bidiyo Shugaban na Falasɗinu ya gabatar da jawabinsa, kuma hakan bai hana shi caccakar Isra’ila ba tare da samun jinjina daga mahalarta taron.
Za a iya cewa shugabannin ƙasashe musamman na Larabawa da na Musulmai na sa rai kwalliya za ta biya kudin sabulu a wannan karon, saboda a wata ganawar sirri da Trump ya yi da su, ya tabbatar musu cewa ba zai bari Isra'ila ta ƙwace yankin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye ba, yana mai cewa ganawar tasa da su ita ce mafi mahimmanci a duka waɗanda ya zauna da su a Taron na UNGA.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda duk ƙorafi da nuna yatsar a kansa aka fi yi, shi ma ya yi nasa jawabin. Sai dai jim kadan da hawansa mimbarin bayani, sai zauren taron ya kaure da masu yi masa ihu, sannan gomman jami’an diflomasiyya suka fice don nuna fushi da shi.
Netanyahu ya yi ta kuranta kansa da kambama ayyukansa, inda ya yi ikirarin cewa Isra'ila ta yi kutse a wayoyin 'yan Gaza don tilasta musu sauraron jawabin nasa a MDD kai-tsaye.
MDD ta sha suka
Bari mu waiwayi batun mai masauƙin baƙi, wato Majalisar Dinkin Duniya, wadda ita ma ta samu nata rabon na suka daga wajen shugabanni da dama, ciki har da shugaban Amurka Donald Trump, wanda wasu ke gani a matsayin shugaban ‘yan ɓarota na duniya.
Trump ya ce MDD ta gaza wajen samar da zaman lafiya a duniya, kuma tana goyon bayan kwararar baƙin haure ba bisa ƙa’ida ba zuwa Ƙasashen Yamma, waɗanda ya ce suna ganin bone.
Shugaba Volodymyr Zelenski na Ukraine shi ma ya ce rawar da MDD ke takawa ta taƙaita ne wajen fitar da bayanai da ƙudurori, lamarin da ke nuni da gazawarta wajen taimaka wa sauran ƙasashe yadda ya kamata.
Sai Shugaba William Ruto na Kenya wanda bai ƙyale MDD ba a lokacin da ya hau mimbarin jawabi, inda ya ce tana fuskantar ƙalubale mai zurfi kan amincinta.
A hannu guda kuma Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima da Shugaban Kasar Ghana da na Afirka ta Kudu da na Kenya duk sun jaddada buƙatar majalisar ta bai wa Afirka kujerun dindindin a Kwamitinta na Tsaro.
Sai dai a yayin da Shugaba Ruto ya ragargaji Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya, kan rashin adalcin da ya ce suna yi wa Afirka, shi kuwa Kashim Shettima neman a yafe wa ƙasarsa da ma Afirka gabaɗaya basussukan da ake bin su ya yi, “amma fa ba a matsayin sadaka ba, sai dai a matsayin wata hanyar samar da zaman lafiya da wadata da za ta amfani kowa,” in ji shi.
Sauran masu ƙorafi kan wasu lamuran sun haɗa da Shugaban Kasar Indonesia Prabowo Subianto, wanda ya koka kan sauyin yanayi da ke illata ƙasarsa da gaggawa, inda a hannu guda, Donald Trump kuma ya yi watsi da lamarin sauyin yanayin a gaban taron na duniya, duk da cewa batun na daga cikin maƙasudan taron.
Ƙarin wasu abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a taron su ne ɓaramɓaramar da Trump ya yi ta yi lokacin da yake gabatar da jawabi, inda ya dinga saka mutane dariya.
Sai kuma yadda jirgin Netanyahu ya dinga shan kewaye-kewaye a hanyarsa ta zuwa halartar taron a Amurka, inda ya yi ta kakkauce wa bi ta sararin samaniyar Faransa da Sifaniya saboda gudun kar a kama shi.
Sannan kuma an ga yadda masu goyon bayan Falasɗinu suka yi zanga-zanga a kusa da otel ɗin da ya yi masauƙi a New York, da ma wacce aka yi a gaban ginin MDD a lokacin da yake gabatar da jawabinsa.
A ƙarshe an ga yadda ‘yan sanda suka tsayar da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron na ɗan lokaci a kan wani titi a birnin New York, saboda wucewar ayarin motocin Donald Trump, lamarin da ya sa Macron ɗin ya kira Trump a waya cikin zolaya game da hakan.
A yanzu dai a iya cewa bayan shekara 80 da kafuwa, da alama Majalisar Dinkin Duniya za ta sake lale kan gazawarta wajen ɗinke ɓarakar duniya.
Sai dai a zuba ido a gani ko lamarin zai sauya salo zuwa shekaru masu zuwa.