Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabi
DUNIYA
4 minti karatu
Yadda jami'an diflomasiyyar duniya suka fice daga Zauren UNGA yayin da Netanyahu zai yi jawabiJami'an diflomasiyyar duniya sun ƙaurace wa Zauren Taron UNGA a yayin da Netanyahu zai fara jawabi, lamarin da ke bayyana yadda ake ƙara ƙaurace masa saboda kisan ƙare dangin da yake a Gaza.
Delegates walk out as Netanyahu speaks, leaving rows of empty seats at the UN General Assembly. (Photo: TRT World) / TRT World
26 Satumba 2025

Majalisar Dinkin Duniya — Jawabin Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a gaban Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ya gamu da cikas na ficewar dimbin wakilai, lamarin da ya nuna yadda ake ƙara nuna masa wariya a fagen duniya yayin da yakin Gaza ya shiga shekara ta biyu.

Netanyahu ya hau dandalin gabatar jawabi a farkon zaman safiyar a ranar Jumma’a, inda ya yi magana mai sarƙaƙaiya, yana cewa Isra’ila tana cikin yaƙi da ƙasashe bakwai.

Tare da amfani da taswirar bayanai da kuma lambar barkod (barcode), ya zargi wadannan kasashe da rashin goyon bayan Isra’ila. “Wannan ba zargi ne ga Isra’ila ba; zargi ne a kanku,” in ji shi.

Netanyahu ya yi ikirarin cewa sukar da ake yi wa Isra’ila cewa tana kai hare-hare kan fararen hula a Gaza ba ta da tushe na gaskiya.

“Idan akwai mutanen Gaza da ba su da isasshen abinci, to saboda Hamas ce ke sace shi,” in ji shi.

Netanyahu ya musanta cewa akwai wata yunwa da aka tilasta wa mutane a cikin Gaza da ke karkashin takunkumi.

“Hamas tana barazana ga fararen hula a Gaza kuma tana amfani da su a matsayin garkuwa, wanda kafofin watsa labarai na Yamma ke amincewa da shi ba tare da bincike ba,” in ji Firaministan Isra’ila.

Yayin da Netanyahu ya fara jawabi, sai jakadun kasashe da dama suka fara tashi daga kujerunsu suna barin ɗakin taron.

Jakadun Ƙasashen Musulmi, Larabawa, Afirka, da Latin Amurka ne suka fara ficewa, sannan wasu daga Turai suka bi su.

Sai Amurka ce da wasu ƙawayenta daga yankin Pacific, da wasu kasashe kadan suka rage a dakin taron da ya zama tamkar fanko.

Wannan yanayi ya zama wata alama mai karfi ta rashin karbuwar Netanyahu a kasashen duniya.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, Birtaniya, Kanada, Ostareliya, da Faransa sun shiga jerin kasashe fiye da 140 da suka amince da kasar Falasdinu a hukumance.

Wannan sauyi ya karkatar da mizani a Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bar Isra’ila cikin ƙarin fuskantar wariya fiye da kowane lokaci a baya-bayan nan.

Wasu daga cikin mambobin gwamnatin Netanyahu sun bukaci a hade wasu sassa ko dukkan yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila.

Wannan mataki zai iya haifar da rikici da Shugaba Trump, wanda ya shaida wa shugabannin duniya a wannan makon cewa zai hana hakan.

Ko isowarsa New York ta nuna irin matsin da yake fuskanta. Jirgin Netanyahu ya kauce wa sararin samaniyar Turai gaba daya, wata hanya da aka tsara don rage yiwuwar kama shi dangane da hukuncin ICC.

Motarsa ta shiga unguwar Manhattan karkashin tsauraran matakan tsaro, yayin da dubban masu zanga-zanga suka taru a wajen hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya, suna daga tutocin Falasdinu da rera wakoki masu sukar kisan kiyashin Isra’ila a Gaza.

A ciki, Netanyahu ya bayyana amincewar Ƙasashen Yamma da Falasdinu a matsayin “sakamako ga Hamas.” Ya kuma nuna fushinsa musamman ga Iran, yana zargin Tehran da haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin.

Amma a Gaza, wata sabuwar jayayya ta taso. Ofishin Netanyahu ya umarci sojojin Isra’ila su watsa jawabin nasa kai-tsaye a Gaza ta amfani da lasifikoki da aka ɗora a kan manyan motoci.

“A matsayin wani bangare na kokarin yada bayanai, Ofishin Firaminista ya umarci hukumomin farar hula, tare da hadin gwiwar IDF, su sanya lasifikoki a kan manyan motoci a bangaren Isra’ila na iyakar Gaza kawai, da nufin watsa jawabi mai cike da tarihi”na Firaminista Netanyahu a yau a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya zuwa Gaza,” in ji wata sanarwa daga ofishin Netanyahu.

Baya ga martani masu zafi daga shugabannin kasashe da ke adawa da yaƙin Isra’ila a Gaza, rorewar da aka yi daga zauren aka bar kujeru ba kowa yayin da Netanyahu ya fara jawabi, ta nuna tsanantar wariyar da ke nuna wa Isra’ila fiye da kowanne lokaci a wannan makon.