AFIRKA
1 minti karatu
DRC ta yanke wa tsohon Shugaba Joseph Kabila hukuncin kisa
Wata kotun sojoji a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idonsa, bisa samunsa da laifuka, ciki har da laifukan yaƙi.
DRC ta yanke wa tsohon Shugaba Joseph Kabila hukuncin kisa
Joseph Kabila served as DRC's president from 2001 to 2019. / Photo: Reuters
4 awanni baya

Wata kotun soja a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasar Joseph Kabila hukuncin kisa a bayan idonsa, sakamakon samunsa da laifuffuka da suka haɗa da laifukan yaƙi.

Laftanar Janar Joseph Mutombo Katalayi, wanda ya jagoranci kotun ta soja a babban birnin ƙasar, ya bayyana a ranar Talata cewa, an samu Kabila da laifufuka daban-daban, ciki har da cin amanar ƙasa, da laifukan cin zarafin bil'adama, da kisan kai, da fyade, da azabtarwa, da tayar da ƙayar baya.

Kabila ya shafe kusan shekaru ashirin yana mulki kuma ya sauka daga mulki ne kawai bayan mummunar zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.

Tun daga ƙarshen shekarar 2023, Kabila ya koma Afirka ta Kudu da zama, duk da cewa ya bayyana a Goma, wani yanki da 'yan tawaye ke iko da shi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, a watan Mayu.