Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine, ya caccaki Faransa kan yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su "tuna tare da ɗaukar alhakin laifukan da suka aikata” a Nijar tun daga shekarar 1899.
"Tun lokacin da muka fatattaki sojojinsu daga [Nijar] a 2023, gwamnatin Faransa take kitsa wani shiri na ƙarƙashin ƙasa domin wargaza ƙasata," in ji Ali Lamine Zeine a jawabin da ya gabatar a gaban Babban Taron MDD [UNGA] ranar Asabar.
Kazalika ya zargi Faransa da “bayar da horo da kuɗi da kuma makamai ga ‘yan ta’adda” tare da yunƙurin haifar da “rikicin ƙabilanci” a Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel.
Firaministan na Nijar ya ƙara da cewa mahukunta a Paris sun ƙaddamar da wani kamfe na watsa “labaran ƙarya da haddasa husuma” da zummar ɓata ƙasarsa da shugabanninta da hukumominta a idanun duniya.
Lamine Zeine ya shaida wa taron UNGA cewa Faransa tana rura wutar rikicin “siyasa tsakanin ƙasata da kuma wasu maƙotanmu," inda ya ƙara da cewa Faransa tana hana Nijar aiwatar da ayyukan ci-gaba tare da hana hukumomin kuɗinta sakat.
"Wannan ya haɗa da ƙiyayyar da Faransa take nuna mana wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba ta hanyar hana masu son zuba jari na ƙasashen duniya irin su ADB da Asusun Bayar Da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a ƙasarmu," in ji shi.
Ya ce abubuwan da suke faruwa a yankin Sahel, musamman a Nijar, sun samo asali ne sakamakon dalilai da dama.
"Da farko, har yanzu ba a warware batun mulkin mallaka ba. ‘Yan ƙasar Nijar ba su manta da azabtarwa da suka fuskanta ba sakamakon mulkin mallaka. Fitattu daga cikinsu su ne ‘yan mulkin mallaka na Voulet-Chanoine da kuma mamayar soji wadda ta haddasa gagaruman kashe-kashe a Tera, Djoundjou, Doutchi, Konni, Tessaoua da Zinder," a cewar Lamine Zeine.
Babban aikin ‘yan mulkin mallaka na Voulet-Chanoine shi ne ƙwace Yankin Chadi tare da haɗa ƙasashen Yammacin Afirka da Faransa ta mamaye ƙarƙashin tsari guda. An ƙaddamar da shirin ne daga Senegal a shekarar 1898.
Firaministan na Nijar ya ce yana "wayar da kan ƙasashen duniya domin ɗauki mataki game da waɗanna dakarun azabtarwa, waɗanda tun ƙarni na 19 ba a kwance musu ɗamara ba, kuma suna ci gaba da ƙaddamar da yaƙi a ƙasata."