AFIRKA
2 minti karatu
Nijar ta ce tana son ta gina injunan makamashin nukiliya biyu tare da Rasha
Nijar ɗaya ce daga cikin ƙasashen Afirka da Rasha take ƙarfafa dangantaka da su a fannoni ciki har da na tsaro.
Nijar ta ce tana son ta gina injunan makamashin nukiliya biyu tare da Rasha
Afirka ta Kudu ce ƙasa ɗaya tilo da take da tashoshin makamashin nukiliya a Afirka / Reuters
26 Satumba 2025

Jamhuriyar Nijar tana son ta gina injunan makamashin nukiliya biyu da za su iya bayar da megawatt 2,000 na makamashi tare da kamfanin nukiliyar Rasha Rosatom, in ji Ministan Haƙar Ma’adinan Ƙasar Ousmane Abarchi ranar Alhamis.

Abarchi ya ce Nijar tana kuma shirin haɗa kai da Rasha wajen haƙar uranium na ƙasar ta Yammacin Afirka.

"Don Allah, bari mu inganta ma’adinan uranium ɗinmu tare," kamar yadda ya bayyana a wani taron nukiliya a birnin Mosko, inda ya yi magana ta hanyar tafinta.

Shugaban kamfanin Rosatom, Alexei Likhachev ya bayyana shawarwarin a matsayin “masu ɗaukar hankali sosai."

'Muhimmanci ga Afirka'

Nijar ɗaya ce daga cikin ƙasashen Afirka da Rasha take ƙarfafa dangantaka da su a fannoni da dama ciki har da na tsaro.

Bayanai daga ƙungiyar makamashin nukiliya ta duniya sun nuna cewa Nijar ita ce ƙasa ta takwas a cikin jerin ƙasashe masu arziƙin uranium da ake haƙowa a shekarar 2024.

Abarchi ya ce tashoshin nukiliyar da ake shirin ginawa za a gina su ne a ƙarƙashin sa idon hukumar MDD da ke kula da makamashin nukiliya, IAEA.

"E, muna da buri mai yawa, amma wannan na da muhimmanci gare mu. Wannan na da muhimmanci ga nahiyar Afirka gabaɗaya," in ji shi.

Rububin gina tashoshin nukiliya

Afirka Ta Kudu ce ƙasar Afirka ɗaya tilo wadda ke da tashar makamashin nukiliya mai aiki, amma ana kan gina injunan makamashin nukiliya a Masar.

Wasu ƙasashe ma sun gabatar da shirin gia tashoshin makamashin nukiliya ciki har da Ghana da Aljeriya da Ethiopia da Kenya da Moroko da Nijeriya da Rwanda da Sudan.