Ministan Kimiyya da Fasaha na Nijeriya, Geoffrey Uche Nnaji, ya sauka daga muƙaminsa bayan rahotanni sun ce ya yi amfani da ta takardar shaidar digiri ta boge.
Wata sanarwar da mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata, ta ce shugaban ya amshi takardar barin aikin ministan.
“Shugaba ya naɗa Nnaji a muƙamin minista ne a watan Agustan shekarar 2023. Ya ajiye aiki a yau a wata wasiƙa inda ya gode wa shugaban kan damar da ya ba shi ta yi wa Nijeriya hidima,” in ji sanawar.
“Nnaji ya ce abokan adawarsa na siyasa ne ke masa bi-ta-da ƙulli. Shugaba Tinubu ya gode masa kan hidimarsa kuma ya yi masa fatan aheri,” in ji Onanuga.
Matsalar da Nnaji ya fuskanta ta kunno kai ne bayan rahotanni sun ce ministan bai kammala karatun digiri ba a Jami’ar UNN ta Nsukka, wadda ya gabatar da takardar shaidar digirinta a lokacin tantance shi domin ba shi muƙamin minista.
Hukumomi a Jami’ar UNN da ke Nsukka sun ce duk da cewa Geoffrey Nnaji ya fara karatu a jami’ar a shekarar 1981 amma bai kammala karatun digirinsa ba.
Kazalika hukumar da ke kula da yi wa ƙasa hidima ta Nijeriya (NYSC) ta ce ministan bai yi wa ƙasar hidima ba, lamarin da ya sa aka ce takardar shaidar yi wa ƙasa hidimar da ya yi amfani da ita ma ta bogi ce.