NIJERIYA
2 minti karatu
‘Yan Majalisar Wakilan Nijeriya sun soki kudirin Majalisar Amurka kan zargin kisan Kiristoci
‘Yan majalisar sun ce Nijeriya ba ta fuskantar rikicin addini, inda suka bayyana buƙatar ɗaukar matakin diflomasiyya.
‘Yan Majalisar Wakilan Nijeriya sun soki kudirin Majalisar Amurka kan zargin kisan Kiristoci
Nigerian House of Reps / Others
3 awanni baya

Majalisar wakilan Nijeriya ta yi watsi da kaulin da ke bayyana cewa Nijeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro na addini ko wanda gwamnati ke daukar nauyi.

Wannan mataki ya zo ne a matsayin martani ga ƙudirin da aka gabatar a Majalisar Dokokin Amurka a ranar 11 ga Maris din 2025.

Ƙudurin na neman a ayyana Najeriya a matsayin “Kasar da ke da damuwa ta musamman” saboda zarge-zargen aikatawa, amincewa, shiryawa, da take hakkin ‘yancin yin addini.

Da take mayar da martani, Majalisar ta umarci hukumomin gwamnati da abin ya shafa, gami da Ma'aikatar Harkokin Waje, da su tattara da kuma isar da kwararan shaidun da suka saɓa da iƙirarin da aka yi a cikin kudirin na Amurka.

Matakin dai ya biyo bayan ƙudirin da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu ya gabatar na muhimmancin gaggawa ga jama’a, kuma ‘yan majalisar suka amince da shi baki ɗaya.

‘Yan majalisar sun yi korafin cewa Najeriya ba ta fuskantar rikicin addini ko kadan, inda suka jaddada bukatar gaggawa don daukar matakin diflomasiyya don ganin kudurin bai yi tasiri a majalisar dokokin Amurka ba.

Makonni biyu da suka gabata, Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da ikirarin cewa ‘yan ta’adda a Najeriya na yi wa Kiristoci kisan kare-dangi, inda ta bayyana zargin a matsayin “ƙarya, mara tushe, abin kyama, da kuma raba kan jama’a.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce bayyana kalubalen tsaro a Najeriya a matsayin yakin da ake yi da ƙungiyar addini guda, gaskiya babban kuskure ne.

“Irin wadannan ikirari ƙarya ce tsagwaron ta, marar tushe, abar kyama, da raba kan juna.”

Ministan ya bayyana cewa masu tsattsauran ra'ayi na kai hari kan 'yan Najeriya mabiya addinai daban-daban, inda ya kuma bayyana irin ci gaban da sojoji suka samu a yakin da ake yi da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar.