DUNIYA
3 minti karatu
Muradun Ƙungiyar G7 a UNGA sun haɗa da ƙara tallafa wa Ukraine da neman tsagaita wuta a Gaza
Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen G7 sun ce a shirye suke su yi aiki tare da abokan hulɗarsu Larabawa kan shawarar yadda za a sake gina Gaza da samar da zaman lafiya mai ɗorewa ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.
Muradun Ƙungiyar G7 a UNGA sun haɗa da ƙara tallafa wa Ukraine da neman tsagaita wuta a Gaza
Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen G7 sun bayyana damuwa game da "karya dokar" sararin samaniyar Rasha a Estonia, Poland, da Romania. / AP Archive
24 Satumba 2025

Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen G7 sun yi alkawarin ƙara tallafa wa Ukraine, sannan sun yi kira da a samar da agajin jinƙai cikin gaggawa da tsagaita wuta a Gaza, tare da amincewa da kafa sabuwar rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Haiti.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da aka fitar bayan taron da suka gudanar a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York a ranar Laraba, Ministocin Harkokin Wajen Kanada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, Birtaniya, Amurka, da shugaban manufofin waje na EU sun nuna damuwa kan abin da suka kira “abin da ba za a yarda da shi ba” na keta sararin samaniyar Estonia da Poland, da Romania wanda Rasha ke yi.

Sun yi gargaɗi cewa irin waɗannan ayyuka na iya kawo barazana ga tsaron duniya. Sun sake jaddada ƙudurinsu na tabbatar da “zaman lafiya mai ɗorewa da ƙarfafa ƙasar Ukraine da kare ‘yancinta da kuma bunƙasarta,” tare da yin alkawarin ci-gaba da aiki tare da Amurka don samar wa Kiev “tabbataccen tsaro.”

Ministocin sun ce suna tattaunawa kan ƙarin matakan tattalin arziki da za a ɗauka kan Rasha, ciki har da matakan da za su shafi ƙasashen da ke taimaka mata, tare da maraba da tattaunawar da ake yi kan amfani da ƙadarorin gwamnatin Rasha da aka daskarar don tallafa wa Ukraine.

Zaman lafiya mai ɗorewa bisa samar da ƙasashe biyu

Dangane da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, G7 ta jaddada “gaggawar rage wahalhalun da fararen hula ke fuskanta a Gaza ta hanyar samar da agajin jinƙai cikin sauri” da kuma tabbatar da sakin dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su.

Sun sake yin kira da a tsagaita wuta a yaƙin Isra’ila da Gaza, suna mai cewa a shirye suke su yi aiki tare da abokan hulɗa Larabawa kan shawarwari na sake gina Gaza da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa bisa mafita ta ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.

Rundunar Haiti

Game da yankin Caribbean, sanarwar ta yaba da shirin Amurka da Panama na kafa Ofishin Taimako na Majalisar Ɗinkin Duniya don Haiti, wanda zai sauya Rundunar Tallafin Tsaro ta Ƙasashe da dama zuwa sabuwar rundunar da za ta yi aiki da nufin kawar da 'yan daba, tabbatar da tsaron ababen more rayuwa, da dawo da kwanciyar hankali tare da haɗin gwiwar hukumomin Haiti.

Iran da hana yaɗuwar makaman nukiliya

Ministocin sun yi kira ga Iran da ta cika dukkan wajibcinta na nukiliya, ta ci gaba da haɗin kai da Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Duniya, tare da shiga tattaunawa kai-tsaye da Washington don cim ma yarjejeniya mai ƙarfi, mai ɗorewa, da kuma cikakkiya da za ta hana Tehran mallakar makaman nukiliya.

Sun kuma goyi bayan shawarar Birtaniya, Faransa, da Jamus na amfani da tsarin dawo da matakan gaggawa a ƙarƙashin yarjejeniyar nukiliya.

Tsaron Indo-Pacific

G7 ta kuma sake jaddada kudurinta na tabbatar da yankin Indo-Pacific mai 'yanci, tare da adawa da “duk wani yunƙuri na sauya matsayin da ake ciki ta hanyar amfani da ƙarfin tuwo ko tilastawa,” ciki har da yankunan Tekun Gabas da Kudancin China da kuma faɗin Mashigin Taiwan.

Sun sake jaddada goyon bayansu ga kawar da makaman nukiliya a Koriya ta Arewa da kuma warware batun sace 'yan Japan.