Bikin Tagwaye na Igbo-Ora: Yadda wani ƙauye a Nijeriya ya zama hedikwatar 'yan biyu ta duniya
Bikin Tagwaye na Igbo-Ora: Yadda wani ƙauye a Nijeriya ya zama hedikwatar 'yan biyu ta duniya
Bikin Tagwaye na Igbo-Ora ne bikin ‘yan biyu mafi girma da ake yi duk shekara a Nijeriya, inda ake tuna asali, al'adu da aka gada da baiwar haifar tagwaye da garin ke da ita wadda ba a saba gani ba.
6 awanni baya

Tsohon garin Igbo-Ora a jihar Oyo a kudu maso yammacin Nijeriya, a karshen makon nan, ya rikide zuwa wani yanayi mai ban sha'awa na kade-kade, launi, da kulla alaka a yayin da daruruwan tagwaye, da iyalansu, da maziyarta suka taru domin bikin tagwayen Igbo da Ora, taron shekara-shekara na tagwaye a kasar da ke Afirka ta Yamma, wanda ke bikin asali, gado, da baiwar haihuwar ‘yan biyu.

Tun daga yara ƙanana da ke murna sanye da riguna masu kyau zuwa tsofaffin tagwaye da ke sanye da agbada iri ɗaya, yanayin ya cika da murmushi iri ɗaya da dariya iri ɗaya. An cika tituna da kade-kade, raye-raye, da tattakin al'adu, yayin da ake ta dannan kyamarori ba kakkautawa.

Bikin raya al’adu

An kaddamar da bikin a shekarar 2018 ta hanyar hadin gwiwa tsakanin al’ummar Igbo-Ora da gwamnatin jihar Oyo, bikin ya samo asali ne a matsayin wani shiri na yawon bude ido domin baje-kolin baiwar musamman ta haihuwar tagwaye da garin ke da ita.

A yau, bikin ya girma zuwa ɗaya daga cikin fitattun tarurrukan al'adu a Najeriya - cakuduwar nishaɗi, ilimi, da adana kayan tarihi.

Bikin na bana mai taken “Tagwayen Wayar da Kai da Karfafa wa Matasa,” ya tattara tagwaye daga sassan Najeriya da sauran kasashen waje. Manyan titunan garin sun shaida raye-raye tare da kade-kade, inda masu wasan gargajiya suka yin rawa a tare inda suke kamar sake haifar da tagwaye a lokaci guda.

Wasan ƙwallon ƙafa na tagwaye don sada zumunci- inda 'yan wasa iri ɗaya suka fuskanci juna - haka kuma gasar ilimi ta tagwaye ta ƙara wa bikin armashi.

Me ya sa Igbo-Ora ke da tagwaye da dama?

Binciken da aka gudanar sun karfafa shuhurar Igbo-Ora tare da ba shi sunan “Hedikwatar Tagwaye ta Duniya”.

Nazarin kimiyya da masu bincike daga Jami'o'in Benin da Ibadan, da aka buga a cikin Mujallar Nazarin Likitanci ta Dakin Karatu na Kasa na Amurka, ya nuna yawaitar haihuwar tagwaye a garin - kusan haihuwa 45 cikin 1,000 tagwaye ne, idan aka kwatanta da matsakaicin haihuwa 12 a duniya. Ƙididdiga ta gida ta nuna cewa wasu iyalai na iya samun tagwaye 158 aga haihuwa 1,000 da suka samu.

Tun da dade wa, wata almara daga mutanen yankinna alakanta lamarin da ita abincin da ake kira, “ila”, miya da aka yi da ganyen kubewa da doya, wanda aka yi imanin yana haɓaka kwayoyin haihuwa da kuma yin tasiri ga haihuwar tagwaye a tsakanin al’umma.

Amma masu bincike sun yi jayayya da wannan nazariyya kuma sun karkata zuwa ga kwayoyin halitta, wanda suka yi imanin na samun ƙarfafu wa ta hanyar salon jima'i, al'adar auratayya a tsakanin al'umma, wanda mai yiwuwa ya tattara kwayoyin halittar tagwaye a cikin gari guda.

Tagwaye a al’adar Yarbawa

A cikin kabilar Yarbawa, tagwaye (wanda aka fi sani da ibeji) suna da matsayi mai tsarki. Ana kallon su a matsayin masu dauka da yada haihuwa, albarka da arziki da kariya daga Ubangiji.

Sunayen tagwaye na ɗauke da ma'ana mai zurfi: ɗan fari shi ne Taiwo - ma’ana "wanda ya ɗanɗana duniya" - yayin da na biyu, Kehinde, ma’ana "wanda ke zuwa daga baya", an yi imani da shi ne ruhin da ya aika Taiwo zuwa gaba. Wannan falsafar tana nuna ra'ayi na duniya inda jerin haihuwa ba shi da muhimmanci kamar kaddara.

Bikin na wannan shekara ya kawo cikar kwari a gidajen otal-otal da masaukan baƙi makonni tun kafin a fara ruguntsumin; ana iya ganin masu sana’a na sayar da sana’o’in tagwaye; kuma masu sayar da abinci suna jiyar da baki daɗi da abin da ake kira "abincin tagwaye", masu hidimar baƙi, masu bincike, da 'yan jarida daga ko'ina cikin duniya waɗanda suka yi tururuwa zuwa garin, wanda kimiyya, da al’adun bikin suka ja hankalin su.