Wani hari da jirgin sama mara matuki ya kashe akalla mutum 30 a wani sansanin 'yan gudun hijira a birnin Al-Fasher da ke yammacin Sudan a ranar Asabar, kamar yadda wata kungiyar masu fafutuka ta bayyana.
Kwamitin gwagwarmaya na Al-Fasher ya ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari a sansanin 'yan gudun hijira na Dar al-Arqam da ke cikin harabar wata jami'a.
Kwamitin ya bayyana cewa gawawwaki sun makale a cikin ramin karkashin kasa, yana mai bayyana lamarin a matsayin "kisan kiyashi" tare da yin kira ga al'ummar duniya su shiga tsakani.
Kwamitocin gwagwarmaya na yankin su ne masu fafutuka da ke hada kai wajen bayar da agaji da kuma rubuta rahotanni kan munanan abubuwan da ke faruwa a rikicin Sudan.
‘Gawawwaki jibge a fili’
RSF tana cikin yaki da sojojin gwamnatin Sudan tun watan Afrilu na 2023. Wannan rikici ya kashe dubban mutane, ya raba miliyoyi da muhallansu, kuma ya jefa kusan mutum miliyan 25 cikin yunwa mai tsanani.
Al-Fasher shi ne babban birnin jiha ta karshe a yankin Darfur mai fadi da ya ki fadawa hannun RSF, ya zama sabon filin yaki mai muhimmanci yayin da dakarun RSF ke kokarin karfafa ikon su a yammacin kasar.
Masu fafutuka sun ce birnin ya zama wurin da “gawawwaki suke jibge a fili" waɗanda na farar-hula ne masu fama da yunwa.
Kusan watanni 18 bayan fara yi a birnin Al-Fasher ƙawanya da RSF ta yi, birnin - wanda ke ɗauke da mutum 400,000 waɗanda suka maƙale - kusan komai ya soma ƙarewa.
An rufe wuraren sayar da miya
Abincin dabbobi da iyalai suka dogara da shi tsawon watanni ya yi karanci kuma yanzu ana sayar da shi a kan daruruwan daloli kowace jaka.
Yawancin gidajen abinci na birnin sun rufe saboda rashin abinci, kamar yadda kwamitocin gwagwarmaya na yankin suka bayyana.