SIYASA
2 minti karatu
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya mutu a India
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya mutu a wani asibitin India, a cewar ‘yan sanda da hukumomin ƙasar.
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya mutu a India
Gwamnatin kasar Kenya ta tabbatar da mutuwar tsohon Shugaban Kasa, Raila Odinga / Reuters
15 Oktoba 2025

Madugun ‘yan adawan Kenya kuma tsohon Firaministan ƙasar Raila Odinga ya mutu a India, kamar yadda wasu kafofin watsa labarai a ƙasashe India da Kenya suka ruwaito daga majiyoyin asibiti da na ‘yan sanda.

Odinga, mai shekara 80, wanda ya je Koothattukulam a gundumar Ernakulam ta Kerala domin jinyar gargajiya mai suna Ayurve, ya mutu ranar Laraba sakamakon bugun zuciya, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Press Trust na India ya ruwaito daga ‘yan sanda da hukumomin asibiti.

Kaasar Kenya ta tabbatar da mutuwar tasa a hukumance, inda gwamnati ta fitar da sanarwar rashin.

Odinga ya faɗi ne yayin irin tattakin nan na safiya a cikin wani asibitin gargarjiya na Ayurve, kuma nan take aka garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa a Koothattukulam, inda aka bayyana cewa ya mutu da misalin ƙarfe 9.52 na safiya, kamar yadda wani mai magana da yawun asibitin gargajiya na ido na Ayurve ya shaida wa Press Trust ta India.

Wasu shugabannin Afirka sun fara tura saƙonnin ta’aziyyarsu inda Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa shafinsa na X cewa: “A madadin gwamnatin Ethiopia, ina miƙa ta’aziyyata game da rasuwar tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga. Allah Ya sa ya huta.’’

‘Bugun zuciya’

Kafofin watsa labaran India sun ba da rahoton cewa Odinga, wanda yake jinya a birnin Kochi da ke kudancin India, ya samu bugun zuciya ranar Laraba  kuma aka garzaya da shi asibiti, inda aka bayyana cewa ya mutu.

A matsayinsa na jagoran ‘yan adawa, Odinga ya sha kaye a dukkan takarar shugaban ƙasa biyar da ya yi inda biyu daga cikin zaɓukan suka janyo rikici.

Aikinsa a matsayin mai gwagwarmayar dimokuraɗiyya cikin shekarun da suka wuce ya taimaka wajen samar da muhimman gyararraki biyu na ƙasar: dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da yawa a shekarar 1991 da kuma sabon kundin tsarin mulki a shekarar 2010.

Ya jagoranci jerin zanga-zanga bayan zaɓen 2007 mai cike da ce-ce-ku-ce da ya jefa ƙasar cikin rikici mafi muni tun bayan da ta samu ‘yancin kai. Kimanin mutum 1,300 ne aka kashe kuma aka raba dubban mutane da gidajensu.