AFIRKA
3 minti karatu
'Yan Kamaru na kaɗa ƙuri'a a zaɓen da Paul Biya ke neman wa'adi na takwas
’Yan takara 13 ne suke neman maye gurbin Shugaba Biya ciki har da wasu da suka taɓa kasancewa na hannun damansa a shekarun baya.
'Yan Kamaru na kaɗa ƙuri'a a zaɓen da Paul Biya ke neman wa'adi na takwas
’Yan takara 13 ne suke neman maye gurbin Shugaba Biya ciki har da wasu da suka taɓa kasancewa na hannun damansa a shekarun baya. / Reuters
12 Oktoba 2025

A yayin da ’yan ƙasar Kamaru ke fita rumfunan zaɓe a ranar Lahadin nan domin kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa, shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya Paul Biya yana son al’ummar ƙasar su sake zaɓarsa domin yin sabon wa’adin shekara bakwai.

Mutum fiye da miliyan 8.2 ne suke da rajistar zaɓe a ƙasar Kamaru wacce take da yawan jama’a da ya wuce mutum miliyan 30. Kuma batun tattalin arziki da rashin aikin yi da matsalar tsaro su ne suka fi mamaye yaƙin neman zaɓen.

Mista Biya na Jam’iyyar Cameroon People’s Democratic Movement (RDPC), wanda a bana yake da shekara 92, ya fara mulkin ƙasar ne tun shekarar 1982, kuma bana yana neman wa’adi na takwas ne a jere.

Idan shugaban ƙasar ya samu nasara a babban zaɓen na ranar Lahadi, zai ci gaba da kasancewa a kan mulki har zuwa lokacin da zai kusa cika shekara 100 a duniya.

Maye gurbin Biya 

’Yan takara 13 ne suke neman maye gurbin Shugaba Biya ciki har da wasu da suka taɓa kasancewa na hannun damansa a shekarun baya.

Daga cikin manyan ’yan takara akwai Issa Tchiroma Bakary wanda ya taɓa kasancewa mai magana da yawun gwamnatin Biya kuma ministan ayyuka.

Bakary, mai shekara 76, ya sauya sheƙa zuwa ɓangayen ’yan hamayya, inda ya ce yana tare da matasa kuma yana goyon bayansu.

Tsohon ministan yana takara ne ƙarƙashin Jam’iyyar Cameroon National Salvation Front wacce aka kafa a shekarar 2007.

Tsohon Firaiministan Ƙasar a shekarar 1982 kuma wani wanda ya taɓa kasancewa na ƙut da ƙut da Mista Biya, Bello Bouba Maigari, shi ma yana takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen bana.

Fitaccen ɗan siyasar mai shekara 78 ya taɓa fafatawa da Shugaba Biya a baya amma bai yi nasara ba.

Cabral Libii, mai shekara 45, shi ne ɗan takarar da ya fi karɓuwa a tsakanin matasa wanda tsohon mai gabatar da shirye-shirye a wani gidan radio kuma malamin jami’a ne.

Cabral wanda ya zo na uku a zaɓen da aka yi a ƙasar a shekarar 2018, yana yawan cewa yana cikin tafiyar matasa wacce za ta samar da sabuwar ƙasar Kamaru.

Sannan akwai Joshua Osih, mai shekara 56, wanda yake takara a babbar jam’iyyar adawa a Kamaru wato Social Democratic Front.

Joshua ya ce idan aka zaɓe shi, zai kawo ƙarshen rikicin ’yan aw-are na yankin da ke magana da Turancin Ingilishi cikin kwana 100.

Sai dai akwai wani cikin manyan ’yan hamayyar da hukumar zaɓen Kamaru ta haramta wa yin takara a zaɓen wato Maurice Kamto.

Maurice ne babban abokin hamayyar Shugaba Biya a zaɓen shekarar 2018.

Ana gudanar da babban zaɓen ne wata ɗaya bayan ɗaya daga ’ya’yan Shugaba Biya ta wallafa wani bidiyo a shafin TikTok inda ta buƙaci ’yan Kamaru da kada su zaɓi mahaifinta.

Ta ce “mutane da yawa sun sha wuya” ƙarƙashin mulkinsa

.Ko da yake Shugaba Biya ya kafe cewa shi ne ya fi duka sauran ’yan takarar cancanta, inda yake cewa zai ci gaba kawo wa ƙasar ci gaba ta kowane fanni.

Shugaba Biya wanda aka daɗe ba a gan shi a bayyanar jama’a ba, ya bayyana a wajen yaƙin neman zaɓensa a garin Maroua a ranar Talata, inda ya sha alwashin magance matsalar tsaro da rashin aikin yi.