Taimako ya yi ƙaranci a yayin da ‘yan Sudan ta Kudu ke fama da tagwayen rikici
AFIRKA
5 minti karatu
Taimako ya yi ƙaranci a yayin da ‘yan Sudan ta Kudu ke fama da tagwayen rikiciJama’ar Sudan ta Kudu da aka raba da matsugunansu kuma suke fama da rikici da illolin sauyin yanayi na gwagwarmayar sake gina yankunansu cikin juriya a yayin da suke fuskantar sabon rikici, ambaliyar ruwa da taimakon da ba ya isa.
A 'yan makonnin nan, koguna da suka cika sun lakume yankuna da dama na noma da gidajen zama. Hoto: UNHCR/Tiksa Negeri / Others
6 awanni baya

Adhieu Marial na tsaye a gaban ɓaraguzan gidanta da ke jihar Unity ta Sudan ta Kudu, tana duba irin abubuwan da ambaliyar ruwan ta rage mata.

"Na farko, mun gudu daga bindigogi. Yanzu, muna gudu wa daga ruwa," mahaifiyar 'ya'ya hudu ta shaida wa TRT Afrika.

A 'yan makonnin nan, koguna da suka cika sun laƙume yankuna da dama na noma da gidajen zama a jihohin Jonglei, Upper Nile da Unity, lamarin da ya raba sama da mutane 100,000 da muhallansu.

Wasu da dama sun fara sake gina rayuwarsu ba da jima wa ba bayan an tilasta musu tsere wa tashin hankalin da ya barke a farkon wannan shekarar.

A yanzu kuma, ambaliyar ruwa na sake jarrabar su.

Adhieu, daga cikin waɗanda ke fafata wa don ci gaba da kasancewa a cikin wani bala'i, ta yanke shawarar mayar da hankali kan makoma. Ibtila’o’i da suka afku a baya sun koya mata abin da kawai ke aiki lokacin da ba ku da wani abu da za ku rasa ita ce juriya.

"Ambaliya ta mamaye gidanmu, amma muna ci gaba da sa rai. Tare da wadannan tantuna na robar filastik da hukumomin agaji ke rarrabawa, akalla muna da dan karamin matsuguni.

“'Ya'yana suna cikin koshin lafiya a yanzu. Muna dora kafafunmu a kan wannan karamar busasshiyar kasa, kuma za mu sake gino rayuwa daga farko.

“Dole ne mu yi hakan," in ji Adhieu, tana mai bayyana ra'ayin dubban mutane da ke kokawa don sake gina rayuwarsu daga farko.

Yamutsattsen rikici

A kowace rana, a jihohin Sudan ta Kudu da ambaliyar ruwa ta yi tagayyara wadanda suka rasa matsugunansu da jin dadin rayuwarsu na fuskantar jarrabawar neman hanyar sake gina rayuwarsu daga farko.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa idan aka ci gaba da samun ambaliyar ruwa, za a iya raba mutane 400,000 da muhallansu nan da karshen shekara.

Ana sa ran kololuwar mamakon ruwan sama nan da makonnin karshe na watan Oktoba, wanda hakan ke barazanar ta'azzara karancin abinci.

"Muna shaida guguwar sauyin yanayi da tashe-tashen hankula, inda wani rikici zai kaure tare da yumutse wa da wani rikicin," Eunice Njeri, wata jami'a da ke aiki da kungiyoyi masu zaman kansu a Sudan ta Kudu, ta shaida wa TRT Afrika.

"Wani iyali da rikici ya raba da muhallansu sun isa wani sabon yanki, amma nan da nan ambaliyar ruwa ta sake raba su da muhallansu na nan wajen.

“Wannan abu na yau da kullum yana ruguza hanyoyin tallafa wa al'umma, ya mamaye ayyukan yau da kullun, kuma yana haifar da mummunan yanayi mai rauni wanda ke da wuyar magance wa."

Njeri ta yi nuni da cewa mafita ta ta'allaka ne a cikin hadaddun dabaru don rage kowane irin radadi, maimakon ɗaukar su a matsayin matsaloli daban-daban. "Matakin kasa da kasa dole ne ya kasance mai hadin kai da juna kamar yadda rikice-rikicen suke," in ji ta.

Ilimi a matsayin ginshiki

A yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubale, wani al'amari mai daɗi mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa shi ne imaninsu marar rawa ga ƙarfin iliminsu a kokarin kalubalantar ibtila’in.

Malamai sun kuduri aniyar ci gaba da tafiyar da harkokin ilimi duk da cewa makarantu da ajujuwa sun koma kamar tafkuna.

"Wannan shi ne babban kalubalenmu," in ji Puot Kuol, malami a Upper Nile. "Amma ba za mu iya mika wuya ba. Yakin ya kawo tsaiko ga harkokin iliminsu, kuma yanzu ambaliya ta sake haifar da wani kalubalen.

“Amma muna neman mafita - koyarwa a karkashin inuwar bishiya, a cikin wani tanti da aka bayar, a ko'ina za mu iya. Wadannan yaran su ne makomar Sudan ta Kudu. Za mu nemo hanyar koyar da su."

Ra'ayin Puot ya kwatanta yadda al'ummomin yankunan Sudan ta Kudu suka kuduri aniyar sake gina wa, koyo da kuma kwato makomarsu ba tare da wata matsala ba.

Gibin kudaden tallafi

Hukumomin agaji suna karfafa wannan juriyar, tare da samun UNHCR da abokan aikinta suka ba da fifikon taimakon ceton rai ta hanyar bayar da tsabar kudi, matsuguni na gaggawa da tabarmi.

Suna kuma yin aiki akan daukar matakai na dogon lokaci kamar tura famfunan ruwa da gyara manyan magudanan ruwa. Wadannan yunƙurin sun kankama tsawon shekaru biyar don taimaka wa al'ummomi jure rikice-rikicen yanayi da ke maimaitu wa.

Amma duk da haka kiran kasa da kasa na tallafa wa Sudan ta Kudu na da karancin samun kudade, sabanin babban rikicin da ke bukatar karin kudade.

Matakan tallafin kudade na yanzu suna ba wa UNHCR damar taimaka wa kashi ɗaya bisa uku na mutanen da za su yi gudun hijira a wannan shekara, wanda ya tilasta wa hukumar rage ayyukan da ake yi a yankunan da abin ya shafa kamar jihar Unity.

Amma ga wadanda ke kan sahun gaba, duk wata shimfida ta robobi, kowace hanyar ruwa babba da aka gyara da kowane ajujuwa na wucin gadi, nasara ce a kan matsalar.