Wilma Nchito ta koyar da zane-zane na shekaru talatin, tana gabatar da zamanin ɗalibai daban-daban zuwa ƙwararrun kimiyya da ke yin taswira waɗanda ke bayyana wurare da fasalin sararin samaniya daidai.
Za ta waiwaya baya cikin alfahari da gamsuwa da aikinta na tsawon lokaci har sai da ta hadu da wani faifan bidiyo a yanar gizo shekaru kadan bayan ta yi ritaya wanda ya girgiza tushen fannin da ta kware a kai.
Bayanan da ke cikin faifan bidiyon sun nuna cewa taswirar duniya da ta dogara da ita a tsawon aikinta na koyarwa na da babban aibu, wanda ke jirkita sunan Afirka a matsayin nahiyar da ba ta da kasashe da yawa.
"Ina tunanin kusan shekaru shida ko bakwai da suka gabata ne. Bayan abin da na gani, na ji irin cewa kamar, 'Tsaya na minti daya', Nchito ta shaida wa TRT Afrika. "A matsayina na mai zana taswira, na ji haushi."
Bidiyon ya nuna yadda ƙasashen da aka bayyana na da girma fiye da Afirka akan taswirori na yau da kullun za su iya shiga cikin nahiyar tare da zama a ciki. Abin ya zama kamar yadda Nchito ta yarda, gaskiya a bayyane da ake boye ta karara.
Tsinkaye bisa kuskure
Hasashen Mercator, wanda aka ƙirƙira a ƙarni na 16 kuma har yanzu yake matsayin taswirar duniya da aka fi amfani da ita, ya rage girman Afirka ta hanyoyi fiye da ɗaya.
Nahiyar tana da fadin murabba'in kilomita miliyan 30.3, ta biyu wajen girma bayan nahiyar Asiya mai girman mrabba’in kilomita miliyan 44, kuma ta fadadu zuwa yankuna shida na lokaci. Kasashe 30, ciki har da Amurka, India, Japan, China, Iraki da yawancin Turai, na iya shiga cikiniyakokinta.
Duk da haka, a taswirar Mercator, nahiyar ta zama karama, kasa da yawancin waɗannan ƙasashe daidaiku.
"Girman taswirar Afirka ba daidai ba ne," in ji Moky Makura, babban daraktan Africa No Filter. "Wannan ne gangamin ɓarna mafi dade wa a duniya, kuma ya kamata ya dakata haka."
Don haka, ta yaya ƙwararrun masu zane-zane kamar Nchito suka kasa gano wannan shekaru da yawa? Ta zargi tsarin ilimi na mulkin mallaka da rashin gaskiya a cikin zane-zane na Afirka.
"Wannan shi ne gaskiya mai daci game da tarihinmu na mulkin mallaka. Iliminmu na mulkin mallaka ne.
“Littattafan da na karanta don samun horo kan zane-zane ba mu muka rubuta su ba. Ee, za su ambaci gaskiyar, amma tana boye a fili. Mun koya a matsayin masu zane-zane kuma muka koyar da cewa tsinkayen ba ya nuna ainihin girman, "in ji Nchito.
Hanyoyin fasaha na zana taswira suna ba da kariya ga waɗannan aibu na tale-tale.
Lokacin da kuka canza yanayin taswira mai bangarori uku zuwa mai kusurwa biyu, babu makawa a samu jirkita gaskiya. Masu zane-zanen taswira sun san wannan, ku koya wa sababbin ɗalibai, kuma ku ci gaba da ayyuka.
Makaman yada farfaganda
Wannan jirkita gaskiya na Mercator ba wai arashi ba ne ko kuskuren lissafi.
Farfesa Murat Tanrıkulu, malamin ilimin kasa a jami'ar Cankırı Karatekin ta Turkiyya, ya bayyana taswirori a matsayin kayan aikin farfaganda a tsawon tarihi.
"Akwai lokuta a tarihi da aka yi amfani da taswira don yin ƙarya," in ji Nchito. "Yin karin girman yankin da wata kasa ta mamaye na daya daga cikin irin wadannan karairayi.
“A nahiyar Afirka ban san ko da gan-gan aka yi ba, amma gaskiyar magana ita ce ana iya amfani da taswirori don ci gaba da yin karya."
Tanrıkulu ya bibiyi sha'awar zane-zanen yammacin Afirka ga fitaccen shugaban kasar Mali Mansa Musa da ya yi tafiya mai cike da tarihi zuwa Makka a shekarar 1324.
"Akwai mutane 60,000 a tawagar wannan tafiya, 2,000 daga cikin su sojoji ne. Akwai rakuma tamanin kowanne dauke da kilo 300 na zinare. Jimillar zinare tan 24,530 kenan," in ji shi.
Labari ya bazu kan Mansa Musa yana rabon zinare yayin da shi da mukarrabansa ke bi ta garuruwan da ke kan hanyar Mali zuwa Saudiyya. Daga nan sai masu zane-zane na yammacin Turai suka fara ƙirƙirar abin da aka sani da "Taswirar Mansa Musa".
Tanrıkulu ya ce "A daya daga cikin zanen da aka yi, an nuna Musa da sandar zinare kuma yana zaune a kan wata karagar mulki ta zinare."
Ana nuna 'yan kasuwa suna tafiya zuwa gare shi, dukiyar ce ke jan hankulansu. "Ba zato ba tsammani Afirka ta zama sananniya kuma abu na gaba shi ne mamaye nahiyar, kama wa da kuma sace arzikin nahiyar," in ji malamin ilimin yankunan.
Babban Taron Berlin na 1884 ya kawo abin da Tanrıkulu ya kira "rarraba Afirka cikin lumana tsakanin ‘yan uwa na Yammacin Duniya".
An yi aiki sosai na zana taswira - na mulkin danniya da na mulkin mallaka - kafin a kama Afirka cikin sauri.
Yayin da nahiyar Afirka ke karkashin ikon Turawa, taswirar Mercator ta kara karfafa siyasa da tattalin arziki na kasashen da suka yi wa mulkin mallaka a nahiyar, inda suke murƙushe murya da danne karfin nahiyar a duniya.
Sakamako na dogon lokaci
Jirkita gaskiyar ba wai ta alamu ba ce kawai.
"Ina tunanin hakikanin abin da ke tattare da shi shi ne, idan kuna mu'amala da wani abu da ya fi shi girma, su ne manufofinku da zuba jarinku na da tasiri, saboda kuna dogara ne akan bayanan da ba daidai ba," in ji Makura.
Gangamin da ake ci gaba da yi na "Corect The Map" *Gyara Taswirar), wanda kungiyoyin Africa No Filter and Speak Up Africa ke jagoranta, yana tura ƙungiyoyi don yin amfani da taswirorin da ke nuna ainihin girman ƙasashen.
"Muna aiki tuƙuru don inganta manhaji inda tsinkayen Duniya Daidaitacciya zai kasance babban ma'auni a cikin ajujuwa," in ji Fara Ndiaye, wadda ta kafa kungiyar Speak Up Africa.
Tana fatan cibiyoyin duniya, gami da na Afirka, za su yi amfani da wannan tsinkayen.
Ba'amurke ɗan wasan kwaikwayo Tom Patterson ne ya kirkiri batun Hasashen Duniya Daidaitacciya a 2017. Ya dinga kawo asalin girman da aka watsar tare da siffa da take jirkitacciya.
"Kamar yadda aka koya mana cewa Mercator bai nuna girman da ya dace ba, dole ne mu ce Patterson bai nuna siffar da ta dace ba, amma girman ya yi daidai," Nchito ta shaida wa TRT Afrika.
Selma Malika Haddadi, mataimakiyar shugabar hukumar Tarayyar Afirka, ta ce hasashen Mercator ya haifar da ra'ayin karya da ke cewa Afirka ta kasance "daga gefe guda" duk da kasancewar ta nahiya ta biyu mafi girma a duniya, da sama da mutane biliyan daya ke zaune a cikin ta.
"Zai iya zama kamar taswira ce kawai, amma a zahiri, ba haka ba ne," Reuters ta rawaito ta tana fadin hakan. "Kungiyar Tarayyar Afirka tana goyon bayan wannan gangami, wanda ke da alaƙa da manyan manufofinmu na maido da martabar Afirka a fagen duniya, ƙalubalantar labaran wasu game da nahiyar da haɓaka ingantaccen wakilci mai daidaito na nahiyar."
Tasiri a kwakwalwa
Nchito ta mayar da aikinta na bayan ta yi ritaya da rubuta littafin karatun sakandare da ke magance jirkita gaskiya.
"Kana fara mataki na 1 sai a ce maka kai karami ne kuma ba ka da amfani. Ka girma, ka yi makarantar sakandare, mutane suna ci gaba da ce maka karami ne, kuma suna nuna maka hotunan wadanda suka fi ka girma. Hakan zai dasu a cikin zuciyarka kuma ka fara yarda da wannan rashin gaskiya," in ji ta.
"Ba wai kawai mutanen da ke kusa da ku sun yarda cewa kai karami ba ne, kana ɗaukar kanka a matsayin ɗan ƙaramin mutum, kuma kana barin mutane su ɗauke ka a matsayin ƙaramin mutum saboda kuskuren da ake yi. Kuma wannan shi ne abin da ya faru da nahiyarmu. Shekaru da yawa, mun bar mutane su dauki nahiyar kamar kasa ce kwaya daya."
Girman Afirka bai iyakance ga girman kasa kawai ba. Nahiyar na rike da kashi 60% na filayen noma da ba a noma wa a duniya. Jumhuriyar Dimokradiyyar Kongo kadai tana da kashi 52.8% na arzikin Cobalt na duniya. Dangane da rahoton arzikin Afirka na 2025, ana hasashen yawan miloniyoyi na dala zai haura sama da 200,000 a cikin shekaru goma masu zuwa.
Nchito ta yi imanin al'ummar Afirka masu zuwa a nan gaba za su ɗauki kansu daban idan ba a karkatar da ra'ayinsu game da duniya tun suna yara ba.
"A cikin shekaru uku ko hudu masu zuwa, dole ne mu rera wakar, 'Gyara Taswirar'," in ji ta, tana mai kira ga 'yan Afirka da su ba da gudunmawarsu wajen sauya salon ra'ayin duniya game da nahiyar.