AFIRKA
1 minti karatu
Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutane 15 a Ghana
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa kwale-kwalen ya yi lodi ne fiye da ƙima, a cewar hukumomi.
Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutane 15 a Ghana
Mutane 15 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a Ghana kuma galibinsu kananan yara ne: hukumomi / AP
13 Oktoba 2025

Wani kwale-kwale dauke da fasinjoji ya kife a tafkin da ke arewa maso gabashin Ghana, inda ya kashe mutum 15 waɗanda akasarinsu ƙananan yara ne, kamar yadda hukumomin da ke kula da harkokin ruwa suka sanar.

“Abin takaici, mutum 11 daga cikin wadanda suka mutu yara ne ‘yan tsakanin shekaru biyu zuwa shekaru 14 (maza biyar da mata shida)” a hatsarin da ya afku a ranar Asabar a Tafkin Volta da ke gundumar Krachi ta Yamma a yankin Oti, a cewar wata sanarwa da Hukumar da ke kula da ruwa ta Ghana ta fitar a ranar Lahadi.

Yaran da sauran wadanda abin ya rutsa da su wadanda suka kusan kai shekaru 64, suna kan hanyar Okuma zuwa Bovime ne a lokacin da kwale-kwalen ya kife, in ji sanarwar.

Mutum hudu daga cikin manyan sun tsira da ransu, a cewar sanarwar, tana mai bayyana hatsarin a matsayin mai “mai muni kana wanda ya keta ka’idojin tsaro da aka gindaya’’.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa kwale-kwalen ya yi lodi ne fiye da ƙima, a cewar hukumar.

An tura wata tawagar bincike ta musamman, ciki har da sojojin ruwa domin tantance musabbabin lamarin.