Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya ayyana kwanaki bakwai na zaman makoki na kasa baki daya bayan rasuwar jagoran adawa kuma tsohon Firaminista Raila Odinga, tare da sanar da cewa za a yi masa jana'izar ban-girma ta ƙasa.
An ruwaito cewa Odinga mai shekaru 80, ya yanke jiki ya fadi yayin da yake tattaki da safe a cikin wani wurin magani na Ayurvedic da ke Koothattukulam a India. An garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa, inda aka tabbatar da rasuwarsa da karfe 9:52 na safe agogon yankin.
A cikin wani jawabi na kasa da ya yi a ranar Laraba, Shugaba Ruto ya yi wa Odinga jinjina, yana bayyana shi a matsayin “jagora mara tsoro” da kuma dattijo wanda tasirinsa ya tsara yanayin siyasar Kenya tsawon shekaru da dama.
“A cikin girmamawa ga gudunmawar da mai girma Raila Odinga ya bayar ga kasarmu, na ayyana kwanaki bakwai na zaman makoki na kasa, inda tutar kasa za ta kasance a ƙasa-ƙasa a fadin Jamhuriyar Kenya da dukkan ofisoshinmu na jakadanci a kasashen waje,” in ji Ruto.
Sakon ta'aziyya
Shugabannin ƙasashen Afirka da na duniya suna ta aikewa da saƙonnin ta'aziyya ga ƙasar Kenya kan rasuwar Odinga.
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) ya bayyana Odinga a matsayin “babban mutum a siyasar Kenya.”
“Gudunmawar Odinga ta wuce iyakokin kasa. A matsayinsa na Wakilin Musamman na Tarayyar Afirka kan Cigaban Ababen More Rayuwa a Afirka, ya yi aiki tukuru wajen bunkasa shirin hadin kan nahiyar da kuma inganta hanyoyin sadarwa, wanda ya taimaka wajen kafa harsashin Yarjejeniyar Ciniki ta Nahiyar Afirka (AfCFTA) da kuma sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa,” in ji AUC a cikin girmamawar da ta yi masa.
Hukumar ta kara da cewa za ta “ci gaba da tuna da sadaukarwar Odinga na tsawon shekaru wajen tabbatar da adalci, bambancin ra'ayi, da sauye-sauyen dimokuradiyya,” wanda ya bar “tabo mai zurfi ba kawai a Kenya ba, har ma a fadin nahiyar Afirka.”
Haka zalika, Sakatare Janar na Kungiyar Raya Yankin Gabas (IGAD), Workneh Gebeyehu, ya bayyana ta'aziyyarsa, yana yabawa da sadaukarwar Odinga ga dimokuradiyya da manufofin haɗin-kan Afirka.
“A matsayinsa na mai kishin Afirka, ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman dimokuradiyya, adalci, da hadin kai.
“Gwaggwarmayarsa ta tsawon rayuwa don 'yanci da daidaito ta zamo abin koyi ga al'ummomi a fadin Kenya da ma duniya baki daya, tana tunatar da mu cewa jagoranci ba wai game da iko ba ne, amma game da hidima da sadaukarwa,” in ji Gebeyehu.