Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da Madagascar daga cikinta sa'o'i kaɗan bayan da jagoran juyin mulkin soji a ƙasar ya ce za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar.
“Dole a bi tsarin doka maimakon amfani da ƙarfin soji,” a cewar shugaban ƙungiyar AU Mahamoud Ali Youssouf a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, yana mai ƙari da cewa dakatarwar za ta soma aiki ne nan-take.
Shugaba Andry Rajoelina ya tsere daga ƙasar, saboda fargabar tsaron rayuwarsa bayan shafe makwanni ana zanga-zangar ƙin jinin gwamnati mai taken ‘‘Gen-Z’’, wadda ɓangaren soji suka goyi baya kan ƙarancin ruwa da wutar lantarki, kana matakin korar ɗaukacin majalisar gwamnatinsa da ya yi, ya ƙara dagula lamarin wanda ya kai ga kira da ya yi murabus.

Daga wani wuri da ba a bayyana ko ina ne ba, ya yi yunƙurin rusa majalisar dokoƙin ƙasar ta hanyar doka.
Majalisar ta yi watsi da dokar inda ta kaɗa ƙuri’ar tsige shi a ranar Talata.
Jim kaɗan bayan haka ne, Kanar Michael Randrianirina da jiga-jigan rundunarsa ta CAPSAT suka ba da sanarwar cewa sojoji sun karɓe iko, kana aka sanar da rusa yawancin cibiyoyin gwamnati kuma kafa gwamnatin riƙon kwarya.
Kada a ƙara asarar rayuka
Randrianirina ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa nan ba da jimawa ba za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa bayan da babbar kotun tsarin mulkin ƙasar ta gayyace shi da ya yi wannan aiki.
Kazalika, a ranar Larabar ne, ƙungiyar raya ƙasashen kudancin Afirka ta SADC, ta zaɓi wani kwamitin dattawa a wani yunƙuri na kawar da tashe-tashen hankula a ƙasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
Wata sanarwa da shugaban ƙasar Malawi Peter Mutharika, wanda shi ne shugaban ƙungiyar sashen SADC da ke kula da harkokin siyasa da tsaro da kuma haɗin gwiwar tsaro ya fitar ta ce, tsohuwar shugabar ƙasar Malawi Joyce Banda ce za ta jagoranci kwamitin da zai mayar da hankali wajen cim ma zaman lafiya da tattaunawa a ƙasar da ke yankin tsibirin.
"Ba za a ƙara asarar rayuka wani ɗan kasa ba saboda tashin hankalin," in ji Mutharika.