TURKIYYA
2 minti karatu
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
A cikin wani jawabi a taron Kasuwanci da Tattalin Arziki tsakanin Turkiyya da Afirka a ranar Alhamis, Emine Erdogan, ta jaddada muhimmancin rawar da mata ke takawa wajen tsara sabon labarin duniya yayin da ake fama da ƙalubale kamar yaƙe-yaƙe.
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
Emine Erdogan a Taron Kasuwanci da Tattalin Arziki tsakanin Turkiyya da Afirka a ranar Alhamis 16 ga Oktoban 2025 / AA
3 awanni baya

A cikin wani jawabi a taron Kasuwanci da Tattalin Arziki tsakanin Turkiyya da Afirka a ranar Alhamis, Emine Erdogan, ta jaddada muhimmancin rawar da mata ke takawa wajen tsara sabon labarin duniya yayin da ake fama da ƙalubale kamar yaƙe-yaƙe da kisan ƙare-dangi, da sauyin yanayi, da talauci.

“Hakika, duniya na buƙatar sabon labari,” in ji Uwargida Emine Erdogan. “Ina da yaƙinin cewa hanun mata ne zai rubuta wannan labarin. Kowace rana, a sassa daban-daban na duniya, wata mace tana sauya kyakkyawan tunani zuwa abu na gaskiya.

Ta kuma bayyana cewa matan Afirka suna da wani matsayi na musamman a zuciyarta.

Emine Erdogan ta ce duba da jama’arsu masu ƙarancin shekaru, da yadda suke rungumar sassauyawar zamani, da bunƙasar harkar sana’o’i, Turkiyya da Afirka sun fita daban a harkar tattalin arzikin duniya.

Haɗaka tsakanin Turkiyya da Afirka

Da take jawabi yayin taron, mai ɗakin shugaban na Turkiyya ta bayyana cewa, “Ƙaƙƙarfar alaƙar da ke tsakanin ƙasarmu da ƙasashen Afirka tana rikiɗewa zuwa wacce ta shafi kowane ɓangare, ana samun sauye-sauye masu ma’ana waɗanda suke nuna kyakkyawan fata ƙarƙashin jagorancin mata.”

“Kasuwar Sana’ar Hannu da Gidan Ƙungiyar Raya Al’adu da muka kafa don bunƙasa shigar matan Afirka cikin harkokin tattalin arziki, sun yi fice a matsayin ɗaya daga tasirin wannan abota mafi daɗewa,” a cewar Emine.

Ta ƙara da cewa na yi imani cewa wannan gagarumin taron zai bunƙasa ci-gaba da samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen da mata suke fuskanta a yunƙurinsu na dogaro da kai.

Da take magana kan yawan ziyarar da ta ke kai wa Afirka tun daga 2005 lokacin da aka ƙaddamar da shirin alaƙa tsakanin Turkiyya da Afirka, Emine Erdogan ta ce, “na samu damar sanin kasashe 30.”

“A lokuta da dama, na shaida da idona irin yadda matan Afirka suke samun madafun iko, na ga irin hikimarsu da jajircewarsu da kuma yadda suka bayar da gudunmawa a cikin al’ummarsu,” a cewarta.

Ta ce tun a karon farko take da sha’awar haɗin kai da waɗannan jajirtattun mata.

MAJIYA:X/@EmineErdogan