Majalisar Dinkin Duniya ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkumai bayan kasa cim ma matsaya a tattaunawar ƙarshe kan shirin nukiliyarta, inda Faransa, Birtaniya da Jamus suka gargaɗi Tehran kan ɗaukar matakan da za su kara dagula lamarin.
"Sake kakaba takunkuman Majalisar Dinkin Duniya ba yana nufin ƙarshen diflomasiyya ba ne," in ji ministocin harkokin wajen ƙasashen uku na Turai, da aka fi sani da E3, a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa a ranar Lahadi.
"Muna kira ga Iran da ta guji ɗaukar matakan da za su ƙara dagula lamarin, sannan ta koma bin ƙa'idojin da suka zama dole a ƙarƙashin yarjejeniyoyin tsaron da suka shafi doka," kamar yadda suka ƙara da cewa.
Sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman ya samo asali ne daga matakin da ƙasashen uku suka ɗauka a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (Jamus ta hanyar sauran biyun), bisa zargin cewa ƙasar ta karya yarjejeniyar 2015 da aka tsara domin hana ta samar da makamin nukiliya.
Iran ta musanta zargin cewa tana neman ƙera makamin nukiliya.