'Yan jaridar Muryar Amurka (VOA) sun maka gwamnatin Donald Trump da babbar mai ba shi shawara Kari Lake a gaban kotu, inda suka ce rufe gidan rediyon na Amurka da gwamnatin ta yi ba zato ba tsammani ya saɓa wa dokar ƙasa, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.
Shari’ar, wadda aka shigar a kotun tarayya a Manhattan a ranar Juma’a, tana neman a mayar da ma’aikatan gidan rediyon na dindindin fiye da 900 da kuma ma’aikata na wucin-gadi 550 bakin aikinsu.
Wadanda suka shigar da ƙarar sun hada da tsohon shugaban ofishin fadar White House na Muryar Amurka Patsy Widakuswara da kuma Editar jaridar Press Freedom Jessica Jerreat. Kathryn Neeper, wadda babbar jami'a a Hukumar Kula da Kafafan Yada Labarai ta Amurka (USAGM), ita ma ta kai ƙara.
Lake, wadda Trump ya naɗa don kula da USAGM, ta kare matakin inda ta ce: "Ɓarna da zamba da cin amanar aiki sun yi katutu a wannan ma’aikatar kuma bai kamata Amurkawa masu biyan haraji su ɗauki nauyinta ba.”
Tun bayan rufe gidan rediyon, babu wasu labarai da ake wallafawa a shafinsu na intanet haka kuma an ji su shiru a rediyo.