Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum mai suna Bahman Choobiasl, wanda aka yi zargin cewa shi ne wanda ya fi yi wa Isra’ila leƙen asiri a ƙasar, kamar yadda jaridar Mizan, wadda fannin shari’a na ƙasar ke wallafawa ta ruwaito.
Choobiasl ya yi aiki “a muhimman shirye-shirye na hanyoyin sadarwa“ kuma ya riƙa aika bayanai game da “hanyoyin shigo da kayan lataroni,” a cewar Mizan a ranar Litinin.
"Babban dalilin hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad na yin aiki da wanda aka hukunta shi ne na bayar da haɗin kai domin samun bayanan hukumomin gwamnati tare da yin kutse a rumbunan adana bayanai na hukumomin Iran, ciki har da hanyoyin shigo da kayan lataroni," in ji Mizan.
MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran sabbin takunkumai bayan kasa cim ma matsaya a tattaunawar nukiliya
Kotun Ƙolin Iran ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da mutumin ya yi inda ta tabbatar da hukuncin kisa a kansa bisa laifin “cin hanci a duniya,” a cewar jaridar Mizan.
Ƙaruwar zartar da hukuncin kisa
Iran, wadda ta daɗe tana yaƙin-sunƙuru da Isra’ila, ta kwashe shekaru da dama tana zartar da hukuncin kisan kan mutanen da take zargi da yi wa hukumar leƙen asirin Isra’ila Mossada aiki.
A watan Yunin da ya gabata, rikici tsakanin Iran da Isra’ila ya yi ƙamari inda suka gwabza yaƙi kai-tsaye bayan Isra’ila ta kai hare-hare a wurare da dama a Iran, waɗanda ake gani ta yi su ne bayan samun bayanan sirri daga cikin ƙasar.
Adadin ‘yan ƙasar Iran da gwamnati ta kashe sakamakon yi wa Isra’ila aiki ya ƙaru sosai a wannan shekarar, inda bayanai suka nuna cewa a watannin baya bayan nan an kashe aƙalla mutum 10.