Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi shelar ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC), suna masu bayyana ta a matsayin wadda ‘yan mulkin mallaka ke amfani da ita wajen gallaza wa marasa ƙarfi.
Ƙasashen uku da ake mulkin soji sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa inda suka ce ba za su amince da ikon kotun ta Majalisar Dinkin Duniya da ke zaune a birnin Hague ba.
"Kotun ICC ta tabbatar wa kanta gazawa wajen hukunta laifukan yaƙi da laifukan take haƙƙin bil’adama da laifukan kisan kiyashi da kuma cin zali," in ji shugabannin uku.
Kawo yanzu dai kotun ba ta yi ce komai ba game da matakin da ƙasashen uku suka ɗauka.
Ƙasashe uku masu maƙwabtaka da juna sun zargi ICC da kasancewa “wata manuniya ta wariya a hukunci a faɗin duniya."
Ƙasashen uku dai sun fice daga ƙungiyar raya attalin arziƙin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) baya sun zarge ta da kasancewa karyar farautar masu mulkin mallaka.
Kazalika ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar sun ce suna son fitar da "tsare-tsare na cikin gida na tabbatar da zaman lafiya da adalci ".
Ƙasashen uku sun ƙungiayr ƙasashen Sahel mai suna (AES) a taƙaice a lokacin da suka fara samun matsala da ECOWAS .
Kuma suna ƙoƙarin nesanta kansu daga ƙasashen Yamma, musamman ƙasar Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka inda suke ɗasawa da Rasha da ma wasu ƙasashe domin samun taimako na soji.
Ƙasashen na Yammacin Afirka suna fama da hare-hare na mayaƙan da ke iƙirarin Jihadi, ko da yake suna ƙokarin murƙushe su.
Mene ne ikon kotun ICC?
Kotun ICC, kotu ce ta dindindin wadda aka kafa domin hukunta mutanen da suka aikata manyan laifuka da kuma laifukan take hakkin bil’adama. An kafa ta ne domin ta taimaka wa kotun ƙasashen duniya.
Hedkwatar kotun tana a birnin Hague na ƙasar the Netherlands kuma ta hukunta masu manyan laifuka da suka aikata wasu daga cikin kisan kiyashi mafi muni a duniya tun shekarar 2002.
Sai dai kuma ƙasashe masu ƙarfi a duniya irin su Amurka da China da Rasha ba sa cikin ƙasashen da suka yarda da kotun ta ICC domin ba su rattaba hannu kan yarjejeniyar Roma ba, wadda ta kafa kotun.
Kazalika Isra’ila ba ta cikin ƙasashen da suka amince da kotun kuma ba ta yarda da ikon kotun ba.
Duk da haka dai kotun ta nemi a kama shugaban Rasha Vladamir Putin, yayin da Firaministan Isra’ila wanda ƙasashen duniya ke zargi da yi wa Falasɗinawa kisan kiyashi a Gaza ke yawo ba tare da wata matsala ba.
‘Yan Afirka dai sun dade suna ƙorafi cewa kotun ta ICC ta fi mayar da hankali ne kan hukunta shugabannin nahiyar da ma wasu sassan duniya marasa galihu, amma ta ƙyale waɗanda suka aikata manyan laifuka irin su tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair da tsohon shugaban Amurka Goerge Walker Bush waɗanda suka ƙaddamar da yaƙi a Iraƙi bisa ƙa’ida ba.