Shugaban Kamaru, Paul Biya, mai shekaru 92 ya lashe zaɓen shugaban ƙasar karo na takwas da kashi 53.7 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa, a cewar sakamakon da Kwamitin Tsarin Mulki ya sanar a ranar Litinin.
Ɗan takara na adawa kuma tsohon minista, Issa Tchiroma Bakary, ya zo na biyu da kashi 35.2, in ji kwamitin. Tchiroma ya riga ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara kwanaki biyu bayan zaɓen da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba, tare da kiran gudanar da zanga-zanga.
Mutane huɗu sun mutu a ranar Lahadi sakamakon arangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan ‘yan adawa a birnin kasuwanci na Douala in ji gwamnan birnin.
Masu zanga-zanga da aka yi hira da su a kamfanin dillanin labarai na AFP sun ce jami’an tsaro sun fara da amfani da hayaki mai sa hawaye, sannan daga baya suka fara harbi da harsasai.
Tun a makon da ya gabata, magoya bayan Issa Tchiroma, wanda a cewarsa ya samu kashi 54.8 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Biya ya samu kashi 31.3, suka fito kan tituna suna kare ikirarin nasararsa.
Yawancin masana sun yi hasashen cewa Biya, wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa da ke mulki a duniya, zai sake lashe wa’adin shekaru bakwai.
Biya shi ne shugaban ƙasa na biyu kacal da ya mulki Kamaru tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960.








