Dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) a ranar Alhamis sun kai wani sabon hari filin jirgin saman Khartoum na ƙasar Sudan da jiragen yaƙi marasa matuƙa a rana ta uku a jere.
Rahotanni sun bayyana cewa, jirage guda bakwai sun kai hare-hare a filin jirgin saman da kuma wasu unguwanni, lamarin da ya haifar da fargaba da tashin hankali, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Sudan ta rawaito.
An ji ƙarar fashewar abubuwa a filin jirgin, a cewar kafar.
Tun daga ranar Talata rundunar RSF ta ƙaddamar da hare-hare a filin jirgin da kuma wasu mahimman wurare a Jihar Khartoum, kwana guda kafin sake buɗe shi bayan shafe fiye da shekaru biyu a rufe.
A ranar Laraba ne aka samu jirgin farar-hula na fasinja karo na farko da ya sauka a filin jiragen saman.
Ba a samu ɓarna sosai a filin jirgin ba bayan harin na RSF, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa jaridar Rakoba News.
A cewar jaridar, hare-haren baya bayan nan kan mahimman wurare na ƙasar na nuni da “yadda aka samu canji a yanayin rikicin" tsakanin dakarun RSF da sojojin Sudan, daga fafatawa ta ƙasa zuwa amfani da jirage marasa matuƙa a matsayin makamin soji da matsin lamba na siyasa.
Kawo yanzu dai babu wani ƙarin haske daga ƙungiyar 'yan tawayen kan waɗannan rahotannin.
Tun a watan Afrilun 2023 ne sojoji da dakarun RSF a Sudan suke gwabza yaƙi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 20,000 tare da raba miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin yankin.









