AFIRKA
2 minti karatu
Gwamnatin Kamaru ta kama manyan ‘yan adawa ana dab da sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar
Daga cikin wadanda aka kama akwai Anicet Ekane, shugaban jam’iyyar MANIDEM, da kuma Djeukam Tchameni, sanannen jigo a ƙungiyar Union for Change - duka biyun sun goyi bayan takarar Tchiroma.
Gwamnatin Kamaru ta kama manyan ‘yan adawa ana dab da sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar
Ana sa ran san sanar da zaɓen shugaban ƙasar a ranar Litinin / Reuters
10 awanni baya

Hukumomin ƙasar Kamaru sun kama ‘yan siyasa da masu fafutuka kusan 30 da ke da alaƙa da ɗan takarar shugaban ƙasa na adawa Issa Tchiroma, in ji tawagar kamfen dinsa a ranar Lahadi, lamarin da ya ƙara tayar da hankali kafin sanarwar sakamakon zaben ranar 12 ga Oktoba, da za a bayyana a ranar Litinin.

Daga cikin wadanda aka kama akwai Anicet Ekane, shugaban jam’iyyar MANIDEM, da kuma Djeukam Tchameni, sanannen jigo a ƙungiyar Union for Change - duka biyun sun goyi bayan takarar Tchiroma.

Kamen ya faru ne a yayin da ake samun karuwar arangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan Tchiroma a ƙasar da ke tsakiyar Afirka mai arzikin koko da man fetur. Tchiroma ya yi kira kan a gudanar da karin zanga-zangar kasa baki daya a ranar Lahadi da karfe 2:00 na rana agogon GMT.

Ministan cikin gida na Kamaru, Paul Atanga Nji, ya tabbatar a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Asabar cewa an yi wasu jerin kame da ke da nasaba da abin da ya kira “yunƙurin tayar da tarzoma,” ko da yake bai bayyana sunaye ko adadin waɗanda aka kama ba.

Ya ce: “Kiran da wasu ‘yan siyasa da ke da son jarabar mulki domin a yi zanga-zanga ba shakka yana haifar da yanayin rashin tsaro kuma yana taimaka tayar da tarzoma.” 

A cikin wani sakon da Tchiroma ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, ya ƙaryata zargin tayar da tarzoma, yana kuma zargin cewa wasu jami’an gwamnati sun yi ƙoƙarin yin sulhu da wasu daga cikin waɗanda aka kama kafin a tsare su.

Ya rubuta cewa: “Sun ƙi amincewa da tayin ku, yanzu kuma kuna kama su? To, lokacin da kuke neman sulhu da su, ba ‘yan ta’adda ba ne?”

Tchiroma, wanda tsohon minista ne kuma tsohon abokin Shugaba Paul Biya, ya bayyana cewa shi ne ya lashe zaben, kuma ba zai amince da wani sakamako na daban ba.

Zanga-zanga ta barke a wasu birane da dama cikin makon da ya gabata bayan wasu rahotannin sakamakon wucin gadi da kafafen watsa labarai suka bayar sun nuna cewa Biya yana kan hanyar ayyana nasara.

Biya, mai shekaru 92, wanda ya kasance kan mulki a Kamaru tun 1982, kuma shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya a yanzu, zai iya ci gaba da mulki na tsawon wasu shekaru bakwai idan Kwamitin Tsarin Mulki ya tabbatar da nasararsa a ranar Litinin.