Aƙalla mutum 63 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin da ya rutsa da motoci a kan wata babbar hanya a yankin yammacin Uganda, a cewar 'yan sanda.
Lamarin ya faru ne a kan babbar hanyar Kampala zuwa Gulu da daddare, bayan da wasu motocin bas suka yi taho-mu-gama da juna,” a cewar sanarwar da ‘yan sanda suka wallafa a shafinsu na X a ranar Laraba.
Ɗaya daga cikin direbobin ya yi koƙarin kauce wa afkuwar hatsarin amma sai ya yi kan wasu motocin akalla guda hudu, “waɗanda su ma birkinsu ya ƙwace kana suka yi ta hantsulawa,” in ji sanarwar.
“Sakamakon haka, mutum 63 ne suka rasa rayukansu, sannan duk sauran mutanen da ke cikin motocin da hatsarin ya rusa da su da kuma wasu da dama sun jikkata,” in ji ‘yan sandan.
An kai waɗanda suka ji rauni zuwa asibitin Kiryandongo da sauran cibiyoyin lafiya da ke kusa, a cewar sanarwar, sai dai ba ta yi ƙarin bayani ba kan adadin wadanda suka jikkata ko kuma girman raunukan da suka samu ba.