Kwadebuwa tana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar Asabar, inda shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, mai shekaru 83, ke neman wa’adi na huɗu. Ana fafatawa da shi tare da 'yan takara huɗu daga jam’iyyun adawa.
Ouattara, wanda tsohon ma’aikacin banki ne na ƙasa da ƙasakuma mataimakin daraktan gudanarwa na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), ya hau mulki a shekarar 2011 bayan yaƙin basasa na tsawon watanni huɗu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutum 3,000. Ya danganta kansa da kusan shekaru 15 na ci gaban tattalin arziki da kwanciyar hankali.
Yaƙin ya samo asali ne daga rashin amincewa da sakamakon zaɓe na 2010 daga tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo.
Kwadebuwa, wadda ita ce ƙasar da ta fi kowace samar da koko a duniya tana daga cikin ƙasashen da ke samun saurin bunƙasar tattalin arziki a Yammacin Afirka.
Yadda ɗan takara zai yi nasara
Wasu fitattun 'yan takara sun rasa damar tsayawa takara, wanda hakan ya rage ƙalubale ga Ouattara.
Misali, Tidjane Thiam na jam’iyyar PDCI an cire shi daga jerin masu zaɓe saboda yana da takardar zama na ƙasa ta Faransa da Kwadebuwa. Haka kuma, tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo na jam’iyyar PPA-CI an hana shi tsayawa takara.
Jam’iyyunsu ba su tsayar da wasu ‘yan takara ba. Jean-Louis Billon, mai shekaru 61, wanda ya fice daga jam’iyyar PDCI ta Tidjane Thiam, yanzu yana takara a ƙarƙashin jam’iyyar Democratic Congress (CODE).
Mutane da dama suna ganin tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Simone Éhivet Gbagbo, mai shekaru 76, a matsayin abar mamaki a cikin takarar. Ta tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Movement of Capable Generations (MGC) bayan an hana tsohon mijinta Laurent Gbagbo tsayawa takara.
A nasa ɓangaren, Ahoua Don-Mello mai shekaru 67 yana takara a matsayin ɗan takara mai zaman kansa bayan an kore shi daga jam’iyyar PPA-CI ta Gbagbo. Shi tsohon abokin Gbagbo ne na dogon lokaci. Haka kuma, akwai Henriette Lagou Adjoua mai shekaru 66, shugabar ƙungiyar Group of Political Partners for Peace (GP-PAIX).
Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, ya sanar da takararsa mai cike da cece-kuce ta wa’adi na huɗu a watan Yuli bayan ya canza kundin tsarin mulki. Fiye da mutum miliyan takwas ne suka yi rijistar zaɓe. Za a buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 0800 GMT kuma a rufe da ƙarfe 1800 GMT.
Ana sa ran samun sakamakon wucin-gadi cikin kwanaki biyar. Za a gudanar da zaɓen zagaye na biyu idan babu ɗan takara da ya samu fiye da kashi 50% na ƙuri’un.








