An tsinci gawar jakadan Afirka ta Kudu a Faransa, Nkosinathi Emmanuel Mthethwa a wajen Otal ɗin Hyatt, wani gini mai tsawo da ke Porte Maillot a yammacin birnin Paris, kamar yadda jaridar Le Parisien ta ruwaito a ranar Talata.
An gano gawar Nkosinathi Emmanuel Mthethwa a wajen Otal ɗin bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya ɓace a ranar Litinin, kamar yadda masu gabatar da ƙara suka tabbatar wa jaridar Le Parisien.
Ana zaton cewa jakadan mai shekaru 58 ya diro ne daga hawa na 22, amma an ƙaddamar da bincike don gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Shafin intanet na ofishin jakadancin ya bayyana cewa Jakada Nkosinathi Emmanuel "Nathi" Mthethwa ya kasance Ministan Al'adu da Wasanni na Afirka ta Kudu daga 2014 zuwa 2019, sannan daga 2019 zuwa 2023 an ƙara masa kula da harkokin wasanni.
Matar jakadan ce ta sanar da ɓacewarsa bayan ta samu saƙon waya daga wajensa wanda ya tayar da hankalinta, kamar yadda jaridar Le Parisien ta ruwaito.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Afirka ta Kudu ta fitar da sanarwa a ranar Talata, inda ta aike da saƙon ta’aziyya kan rasuwar jakadan.
Sanarwar ta ce an naɗa shi jakadan Afirka ta Kudu a Faranasa ne a watan Disambar 2023 domin ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.