NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kama 'yan ta'adda 450, sun kuɓutar da mutum 180 a Satumba - Hedkwatar Tsaro
Kazalika mai magana da yawun hedkwatar tsaron Nijeriya Manjo Janar Markus Kangye, ya ce dakarunsu sun ƙwato tarin manyan makamai da sauran kayan aiki na 'yan ta'adda.
Sojojin Nijeriya sun kama 'yan ta'adda 450, sun kuɓutar da mutum 180 a Satumba - Hedkwatar Tsaro
Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarunta sun aiwatar da waɗannan ayyuka ne a watan Satumban da ya gabata / Reuters
14 awanni baya

Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarunta da ke aikin wanzar da tsaro a sassa daban-daban na ƙasar sun kama ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga aƙalla 450 a watan Satumba.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Manjo Janar Markus Kangye ya fitar ranar Asabar a Abuja, babban birnin ƙasar.

Manjo Janar Kangye ya ƙara da cewa dakarun nasu sun kuɓutar da mutum fiye da 180 daga hannun masu garkuwa da mutane, yana mai cewa ‘yan ta’adda aƙalla 39 sun yi saranda yayin samamen da aka kai musu.

“A watan Satumba na shekarar 2025, dakarunmu sun kuɓutar da fararen-hula 180 da aka yi garkuwa da su, sun kama ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 450, sannan sun kawar da masu aikata laifuka da dama a samame daban-daban da rundunoninmu suka kai,” in ji Manjo Janar Kangye.

Wuraren da ‘yan ta’adda suke da ƙarfi

Mai magana da yawun hedkwatar tsaron ta Nijeriya ya ce dakarunsu sun ƙama ƙaimi wajen kai samame a wuraren da ‘yan ta’adda suke da ƙarfi a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe daga ranar 23 zuwa 30 ga watan Satumba.

“Dakarunmu sun kai samame a ƙananan hukumomin Konduga, Gwoza, Mafa, Gubka, Monguno, Damboa, Biu, da Kukawa da ke JIhar Borno. Kazalika sun kai samame a ƙananan hukumomin Madagali, Hong, da Mubi South a Jihar Adamawa da kuma Gujba a Jihar Yobe,” a cewarsa.

Manjo Janar Kangye ya ƙara da cewa waɗannan samame sun kai ga lalata sansanonin ‘yan ta’adda da ƙwato manyan makamai da kuma kama masu haɗa baki da su.

Ya ce, :“Sojojinmu sun kawar da ‘yan ta’adda da dama tare da ƙwato makamai da alburusai da abubuwan fashewa, sannan suka lalata sansanoninsu. Kazalika mun kama mutum 21 da ke yi wa ‘yan ta’adda aiki wato infoma.”