Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da shirin rigakafin cututtuka irin su ƙyanda da shan inna da ta kansar bakin mahaifa wato HPV, da kuma wasu cututtukan da ake watsi da su a faɗin ƙasar.
An gudanar da wannan taron ne a ranar Litinin a ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Manufar wannan shiri ita ce a kawar da ciwon ƙyanda zuwa shekarar 2030, ta hanyar ƙarfafa rigakafin yara na yau da kullum, inganta bincike da sa ido kan ɓarkewar cuta, da kuma samar da shirye-shiryen kawar da ƙyanda a asibitoci na matakin farko da kuma amfani da sabbin fasahohi wajen gudanar da ayyuka.
Ana sa ran yara miliyan 16 za su karɓi allurar rigakafi a wannan kamfe, wanda ya ƙunshi yara masu shekaru daga tara zuwa goma sha huɗu da za a yi musu allurar rigakafin.