NIJERIYA
3 minti karatu
Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta rahoton cewa ‘yan bindiga sun ci galaba kan dakarunta a Kwara
A baya bayan nan ‘yan bindiga suna ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan fararen-hula a wasu ƙauyuka na Jihar Kwara da ke tsakiyar Nijeriya.
Rundunar Sojin Nijeriya ta musanta rahoton cewa ‘yan bindiga sun ci galaba kan dakarunta a Kwara
Rundunar sojin ta yi kira ga mutane su ci gaba da taimaka wa soji da bayanai na gaskiya domin taimaka wa ayyukan da suke yi. / AFP
6 Oktoba 2025

Rundunar sojin Nijeriya ta musanta rahotannin da ke iƙirarin cewa ɓarayin daji sun ci galaba a kan dakarunta kuma sun yi awon-gaba da bindigogi masu jigida shida da harsasai fiye da 30,000 a garin Obanla da ke Jihar Kwara a arewa maso tsakiyar ƙasar.

Rahoton dai ya yi iƙirarin cewa ‘yan bindigar sun yi wa dakarun sojin Nijeriya kwanton-ɓauna bayan sun samu bayanai game da harin da za su kai musu.

Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun ƙwace bindigogi masu jigida aƙalla shida da harsasai fiye da 30,000 daga wasu dakarun haɗaka na Nijeriya.

Wata sanarwa da mataimakin daraktan watsa labarai na runduna ta biyu ta sojin Nijeriya Laftanar Kanar Polycarp Okoye ya fitar ranar Lahadi ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara.

Ya ce dakarun bataliya ta 148, a halin yanzu suna aikin kakkaɓe ‘yan ta’adda a yankunan jihohin Kogi da Kwara, kuma sun yi “gagarumar nasara a ayyukansu.”

Okoye ya ce kwanan ne dakarun suka toshe wani wuri a kan iyakar jihohin Kwara da Ekiti, inda suka kashe ‘yan bindiga biyu kuma suka ƙwace sabbin bindigogi biyu ƙirar AK-47.

Sanarwar ta ce, “Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da wani rahoto na ƙarya da yaudara da wata kafar watsa labarai ta intanet ta rubuta inda ta yi iƙirarin cewa ‘yan bindiga sun ci galaba kan dakarun kuma suka yi awon-gaba da bindigogi masu jigida da harsasai fiye da 30,000 a Obanla, jihar Kwara”.

“Saɓanin iƙirarin na jan hankali, dakarun bataliya ta 148 da suke ayyukan kakkaɓe [‘yan ta’adda] a faɗin jihohin Kogi da Kwara sun ci gaba da samun gagarumar nasara. A wata arangamar da suka yi kwanan nan, dakarun sun toshe wani wuri a kan iyakar jihar Kwara da Ekiti, inda suka kashe ‘yan bindiga biyu kuma suka ƙwace bindigogi biyu ƙirar AK-47,” in ji shi.

“Babu lokacin da aka ci galaba a kan sojin, ko kuma masu laifi suka yi awon-gaba da makamai, kamar yadda kafar ta intanet ta wallafa. Rahoton ƙarya ce da aka shirya domin yaudarar mutane da kuma sanyaya gwiwoyin dakarun tsaro masu jarumta da ke aiki tuƙuru domin dawo da zaman lafiya yankin,” in ji sanarwar.

Ta yi kira ga mutane su yi watsi da rahoton su kuma ci gaba da taimaka wa soji da bayanai na gaskiya domin taimaka wa ayyukan da suke yi.

A baya bayan nan ‘yan bindiga suna ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan fararen-hula a wasu ƙauyuka na Jihar Kwara da ke tsakiyar Nijeriya.