NIJERIYA
3 minti karatu
An nemi kotu ta hana Jonathan takara a zaɓen Nijeriya na 2027
Ƙarar da lauyan ya shigar ta sanya hukumar INEC da babban lauyan Nijeriya a cikin waɗanda aka kai ƙararsu.
An nemi kotu ta hana Jonathan takara a zaɓen Nijeriya na 2027
Goodluck Jonathan
7 Oktoba 2025

An nemi wata kotun tarayyar Nijeriya da ke Abuja ta hana tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 da ma ko wane zaɓe a nan gaba.

Kafofin watsa labaran Nijeriya sun ambato wata ƙara da wani lauya, Johnmary Jideobi, ya shigar inda yake neman kotu ta ba da umarnin hana Jonathan gabatar da kansa ga ko wace jam’iyyar siyasa a Nijeriya domin ta tsayar da shi takara a zaɓen 2027 ko ma ko wane zaɓe a gaba.

Jideobi ya kuma nemi kotun ta hana hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) amsa takararsa ko kuma wallafa sunan Jonathan a matsayin ɗan takara tare da neman kotun ta bai wa babban lauyan Nijeriya umarnin tabbatar da bin umarnin kotun.

Ƙarar da lauyan ya shigar ta bayyana hukumar INEC da babban lauyan Nijeriya a cikin waɗanda aka kai ƙarar.

Kazalika a cikin wata takardar rantsuwa da ya gabatar a kotun domin goyon bayan lauyan, wani mutum mai suna Emmanuel Agida, ya bayyana kansa a matsayin “mai goyon bayan bin kundin tsarin mulki da kuma biyayya ga doka kawai.”

Ya ce tun da Jonathan ya ƙarasa wa’adin mulkin marigayi  Shugaba Umaru Musa Yar’Adua kuma ya yi wani cikakken wa’adi bayan ya lashe zaɓen shekarar 2011, ya riga ya ƙarasa wa’adi biyu da kundin tsarin mulki ya ba da damar yi.

Jideobi ya ce ya shigar da ƙarar ne bayan ya karanta rahotanni a kafofin watsa labarai game da shirin da aka ce Jonathan na yi na sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Lauyan ya yi ishara ga sashe na137(3)  na kundin tsarin mulkin ƙasar inda ya ce ƙyale tsohon shugabna ƙasar ya sake takara zai saɓa wa dokar ƙasa.

Ya ce an rantsar da Jonathan ranar 6 ga watan Mayun shekarar 2010 domin kammala wa’adin marigayi Shugaba Yar’Adua, wanda ya rasu ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010. Daga bisani an zaɓi  Jonathan a shekarar 2011 kuma aka rantsar da shi ranar 27 ga watan Mayu, inda ya yi mulki har zuwa shekarar 2015.

“Na san idan mai amsa ƙara na farko ya yi nasara a zaɓen 2027  a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya—wanda na wa’adin shekarar huɗu ne daga shekarar 2027 zuwa  2031—zai zarce shekara takwas wadda ita ce shekara mafi yawa da ta kamata a shubaga ya yi karagar mulki a Nijeriya,” a cewar Jideobi.

Jideobi ya ce ya shigar da ƙarar ne domin kare hakkin al’umma kuma ya nemi kotu ta hana tsohon shugaban takara.

A shekarar 2022 an shigar da irin wannan ƙarar inda mai shari’a Isa Dashen na babbar kotun tarayya a Yenagoa, Jihar Bayelsa ta kori ƙarar saboda rashin makama domin sashe na 137(3) na tsarin mulkin da ya ƙayyade mulki zuwa wa’adi biyu ya fara aiki ne bayan Jonathan ya bar kan mulki.