Babban Daraktan Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Bayo Ojulari, ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa zuwa ƙarshen shekara, ɗanyen man fetur ɗin da Nijeriya ke haƙowa a duk rana zai kai ganga miliyan 1.8.
Ojulari ya bayyana haka ne a ranar Lahadi bayan ya kai ziyara ga Shugaba Bola Tinubu a Legas.
Ya ce ya ziyarci Shugaban ƙasa ne don ya ba shi rahoto kan ayyukan kamfanin NNPCL tun bayan nadinsa a ranar 2 ga Afrilu.
“Tare da wasu gyare-gyaren da muka yi a watan Agusta da Satumba, dukkan su ana sa ran su dawo aiki a wannan watan.
“Muna sa ran kafin ƙarshen shekara za mu kai akalla ganga miliyan 1.8 a rana,” in ji Ojulari.
Rikicin matatar Dangote da PENGASSAN
Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (PENGASSAN) da Kamfanin Man Dangote sun samu saɓani kan zargin korar ma’aikatan matatar ‘yan Nijeriya fiye da 800 tare da maye gurbinsu da ƙwararru na ƙasashen waje.
A ranar 26 ga Satumba, ƙungiyar ta ba da umarni ga membobinta su fara yajin aiki na ƙasa baki ɗaya sakamakon matakin na Dangote.
Bayan kwana biyar, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin bayan Rukunin Kamfanonin Dangote ya amince ya mayar da ma’aikatan da aka kora, bisa shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi.
Ojulari ya nuna ta’aziyya kan asarar da aka yi a cikin ɗan gajeren lokacin da yajin aikin ya ɗauka.
Sakamakon faruwar wannan lamarin, Ojulari ya jajanta game da irin asarar da aka tafka ta ɗan ƙaramin lokaci sakamakon wannan yajin aikin.
“Abin takaici ne yadda rikicin Dangote da PENGASSAN ya jawo yajin aiki. Kamar yadda kuka sani, idan aka yi yajin aiki kuma ma’aikata masu kula da muhimman wurare ba su nan, ba zai yiwu a ci gaba da aiki yadda ya kamata ba.
“A wannan yanayi, mun rasa fiye da ganguna 200,000 a kowace rana da aka jinkirta.
“Haka kuma an rage fitar da iskar gas, kuma yajin aikin ya shafi wutar lantarki ta kusan megawatt 1.2,” in ji shi.
Gwamnatin Tarayya ta sa baki
A ranar 30 ga Satumba, Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Ƙasa, Nuhu Ribadu, ta shiga tsakani domin sasanta rikicin.
An ce taron ya kasance mai albarka, inda ƙungiyar ta yarda da janye yajin aikin, yayin da ma’aikatan da aka kora aka mayar da su.