AFIRKA
2 minti karatu
Ouattara, na Ivory Coast, ya sake lashe zaben shugaban ƙasa karo na huɗu
A mulkin Ouattara abubuwa sun daidaita a Ivory Coast sannan an samu haɓakar tattalin arziki a ƙasar da ke kan gaba a duniya wajen noman cocoa.
Ouattara, na Ivory Coast, ya sake lashe zaben shugaban ƙasa karo na huɗu
Ouattara has since overseen a period of relative stability and steady economic growth in the world's biggest cocoa producer. / Reuters
3 awanni baya

Shugaban ƙasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya samu nasarar lashe wa’adi na huɗu bayan samun gagarumin rinjaye a zaɓen da aka gudanar, kamar yadda sakamakon wucin-gadi da hukumar zaɓe ta sanar a ranar Litinin ya nuna.

Tsohon ma’aikacin bankin ƙasa da ƙasa mai shekaru 83 ya samu kashi 89.77 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa, wanda ke nuna babbar nasara a karo na uku a jere tun bayan zaɓen 2011 wanda ya kawo shi kan mulki.

Tsohon shugaban ƙasa, Laurent Gbagbo, ya ƙi amincewa da shan kaye a wancan zaɓen, wanda ya jawo yaƙin basasa na tsawon watanni huɗu da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 3,000.

Tun daga lokacin, Ouattara ya jagoranci wani lokaci na kwanciyar hankali da kuma ci-gaban tattalin arziki a ƙasar da ke zama babbar mai samar da koko a duniya.

Adadin masu kaɗa kuri’a ya kai kusan kashi 50 cikin ɗari, wanda ya yi kama da zaɓen shugaban ƙasa na 2010 da 2015, amma ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da kashi 80 cikin ɗari na masu kada kuri’a a zagaye na farko na 2010.

Gbagbo da Tidjane Thiam, tsohon Shugaban Kamfanin Credit Suisse, ba su samu damar tsayawa takara ba a wannan shekara saboda dalilai na doka, yayin da sauran ‘yan takarar adawa ba su da goyon bayan manyan jam’iyyun siyasa, wanda ya sa Ouattara ya zama wanda ake ganin zai yi nasara tun farko.