AFIRKA
1 minti karatu
Sudan ta fitar da 'ƙaƙƙarfan gargaɗi' kan yiwuwar albaliya mai tsanani saboda ƙaruwar ruwan koguna
Tun farkon wannan watan, hukumomi sun bayyana cewa fiye da iyalai 21,000 a Sudan sun fuskanci ambaliyar ruwa da ruwan sama mai karfi a jihohi 11 tun daga watan Yuni.
Sudan ta fitar da 'ƙaƙƙarfan gargaɗi' kan yiwuwar albaliya mai tsanani saboda ƙaruwar ruwan koguna
Sudan ta fitar da 'ƙaƙƙarfan gargaɗi' kan yiwuwar albaliya mai tsanani saboda ƙaruwar ruwan koguna / AA
29 Satumba 2025

Sudan ta fitar da gargadi na “jan hankali” kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar da ke kusa da Kogin Nilu, inda aka bayyana karuwar matakin ruwa a manyan kogunan Blue Nile da White Nile.

Ma’aikatar ban ruwa ta Sudan, a ranar Litinin, ta yi kira ga mazauna jihohin Khartoum, River Nile, White Nile, Sennar, da Blue Nile su kasance cikin shiri, domin ambaliyar na iya shafar gonaki da gidaje.

Wasu manoma a jihar River Nile ala tilasta sun sayar da amfanin gonarsu na albasa cikin gaggawa, saboda rahotannin ambaliyar da ta shafi wuraren da ke kasa, wanda zai iya shafar harkar noma, in ji rahoton Associated Press daga Shendi.

Ma’aikatar Ban ruwa ta Sudan ta yi gargadi a ranar Lahadi cewa, an shafe tsawon kwanaki huɗu a jere ana zabga ruwan sama mai ƙarfi, yayin da madatsun ruwa a yankin suke fitar da ruwa mai yawa. An yi hasashen cewa matakin ruwa zai ragu a tsawon makon.

Tun farkon wannan watan, hukumomi sun bayyana cewa fiye da iyalai 21,000 a Sudan sun fuskanci ambaliyar ruwa da ruwan sama mai karfi a jihohi 11 tun daga watan Yuni.