Masar za ta shirya wani ƙasa da ƙasa kan zaman lafiya na ƙasa da ƙasa a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda Shugaba Abdel Fattah el-Sisi da takwaransa na Amurka, Donald Trump, za su jagoranta.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa a daren Asabar ta bayyana cewa taron zai tattaro shugabanni daga ƙasashe fiye da 20.
Manufar taron ita ce “kawo ƙarshen yaƙin Gaza, ƙarfafa ƙoƙarin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, da kuma fara wani sabon mataki na tsaro da kwanciyar hankali a yankin,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan taron “yana zuwa ne bisa hangen nesa na Shugaban Amurka Trump na samar da zaman lafiya a yankin da kuma ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen rikice-rikice a duniya.”
A ranar Laraba Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da mataki na farko na wani shiri mai matakai 20 da ya gabatar a ranar 29 ga Satumba don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da sakin dukkan fursunonin Isra’ila da ke hannun Hamas a musayar fursunoni Falasdinawa kusan 2,000, da kuma janye sojojin Isra’ila daga dukkan yankin Gaza.
Mataki na farko na wannan yarjejeniya ya fara aiki da ƙarfe 12 na rana agogon cikin gida (0900 GMT) a ranar Juma’a.
Mataki na biyu na shirin ya ƙunshi kafa sabon tsarin mulki a Gaza, samar da wata rundunar tsaro da za ta ƙunshi Falasɗinawa da sojoji daga ƙasashen Larabawa da Musulmi, da kuma ƙwace makamai daga hannun Hamas.
Tun daga watan Oktoba na 2023, hare-haren Isra’ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 67,600 a Gaza, yawancinsu mata da yara, tare da mayar da yankin kufai da ba ya zaunuwa.