Hamas ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila ta kai hari kan ayarin jiragen ruwa na jinƙai da ke kan hanyarsu ta zuwa Gaza a matsayin wani laifi na “fashin teku da kuma ta’addanci na ruwa kan fararen-hula," tana mai kira ga "dukkan masu kare ‘yanci a duniya" su yi Allah wadai da harin.
Ƙungiyar ta ce tsangwama a teku na ƙasa da ƙasa tare da kama masu fafutuka da ‘yan jarida, ya kasance "wani aikin tsangwama na cin amana wanda "ya yi ƙari cikin tarihin mai muni na laifukan da Isra’ila ta aikata.”
Ƙungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad ita ma ta fitar da irin wannan sanarwar, inda take bayyana harin a matsayin "fashin teku da kuma tsagwaron take dokokokin jinƙai na duniya,” tana mai ɗora wa Isra’ila "alhakin tsaron masu gudanar da tafiyar" a kan jiragen ruwa.
Allah wadai daga duniya
Francesca Albanese, wakiliyar MDD ta musamman kan yankin Falasɗinun da aka mamaye, ta ce kama masu fafutukar ayarin jiragen jinƙan ya “saɓa wa doka” kuma ta ɗora wa gwamnatocin Ƙasashen Yamma alhakin kasancewa da hannu a ciki.
Gwamnatoci a faɗin Turai sun nuna damuwa.
Faransa ta yi kira ga Isra’ila ta "tabbatar da tsaron waɗanda suke cikin ayarin tare da ba su kariya ta jakandanci".
Ƙasar Switzerland ta ce kowane mataki da aka ɗauka kan ayarin "dole ya mutunta sharruɗan larura da kuma daidai ruwa daidai tsaki yayin da ake tabbatar da tsaron waɗanda suke cikin ayarin."
Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi Allah wadai "cikin kakkausar murya " kan abin da ta kira wani "aikin ta’addanci " da sojin ruwan Isra’ila ta aikata.”
Sifaniya ta ce tana bibiyar lamarin ƙut-da-ƙut inda ofisoshin jakadancin da ke yankin su kasance cikin shirin ko ta kwana.
Belgium ta yi kira ga Isra’ila ta "mutunta dokar ƙasa da ƙasa, ciki har da dokar teku kuma ta kare ayarin jiragen ruwan ".
Ireland ta bayyana hari kan ayarin a matsayin abin "damuwa."
Shugabn ƙasar Ireland Michael Higgins ya ƙara bayani, inda yake bayyana harin Isra’ila da rufe hanyoyin da ta yi a Gaza a matsayin "abin damuwa ga duniya gabaɗaya."
Ya yi gargaɗin cewa tsaron masu fafutuka ya kasance "abin damuwa ga duk ƙasashe" kuma ya alaƙanta lamarin da abin da ya bayyana a matsayin "manufofi na kisan ƙare dangi " a Gaza.