GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Sojojin Amurka sun isa Isra'ila domin sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Kusan sojojin Amurka 200 ne za su taimaka domin sa ido wurin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar. Sojojin za su zauna a Isra’ila ba tare da sun shiga Gaza ba.
Sojojin Amurka sun isa Isra'ila domin sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Wannan tawagar za ta yi aiki a fannoni kamar dabaru, tsaro, sufuri, tsarawa, da aikin injiniya. / Reuters
5 awanni baya

Sojojin Amurka sun fara isa Isra'ila a ranar Asabar domin shiga cikin wata rundunar ƙasa da ƙasa da za ta kula da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda rahotannin kafofin watsa labarai na Amurka suka bayyana.

Cikin rahoton da kafar watsa labarai ta ABC News ta bayar, ta ambato wasu jami'an Amurka guda biyu, inda kafar ta ce kimanin jami'ai 200 na Amurka ne aka tura Isra’ila domin kafa cibiyar hadin gwiwa da za ta sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta. Wannan tawagar za ta yi aiki a fannoni kamar dabaru, tsaro, sufuri, tsarawa, da aikin injiniya.

Rahoton ya ƙara da cewa, sojojin na Amurka za su zauna a Isra'ila kuma ba za su shiga Gaza ba. Aikin su zai kasance karkashin jagorancin shugaban rundunar US Central Command (CENTCOM), Admiral Bradley Cooper, tare da aiki tare da sassan kasashen yankin da ke cikin rundunar.

Shirin matakai 20 na Trump

Wannan tura sojojin ya biyo bayan sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi a ranar Laraba cewa Isra'ila da Hamas sun amince da mataki na farko na shirin matakai 20 da ya gabatar a ranar 29 ga Satumba domin dakatar da yakin kisan kare-dangi a Gaza.

A karkashin yarjejeniyar, Hamas za ta saki dukkan sauran mutanen Isra'ila da take tsare da su a madadin fursunonin Falasdinawa kimanin 2,000, yayin da Isra'ila za ta fara janye sojojinta daga yankin Gaza a hankali.

Mataki na biyu na shirin ya kunshi kafa sabon tsarin mulki a Gaza ba tare da Hamas ba, kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta Falasdinawa da Musulmai, da kuma karshe, kwace makaman Hamas.

Tun daga watan Oktoba na 2023, hare-haren Isra'ila sun kashe kimanin Falasdinawa 67,200, yawancinsu mata da yara, tare da barin Gaza cikin yanayi mara dacewa.