Shekaru biyu na kisan kiyashin Isra'ila a Gaza: Falasdinawa suna shan yunwa da cin-amana
GABAS TA TSAKIYA
9 minti karatu
Shekaru biyu na kisan kiyashin Isra'ila a Gaza: Falasdinawa suna shan yunwa da cin-amanaMatsalar yunwatarwa da tilasta ƙaura da rufe baki da haɗa baki wajen muzgunawa, duka sun tattaru sun haddasa abin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama suka kira "zahirin kisan ƙare-dangi".
Falasdinawa sun yi alhinin rashin 'yan uwansu da aka kashe a wani harin da Isra'ila ta kai. / AA
4 awanni baya

Shekara biyu bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙinta a Gaza, yankin Falasɗinawa ya zama kango, inda al’ummar yankin ke fama da yunwa, sannan an hana ‘yan jarida magana.

Adalcin manyan ƙasashen duniya ya rabu tsakanin masu goyon baya da kuma masu nuna takaici jifa-jifa.

A yaƙin da ya fara tun daga watan Oktoban 2023, Isra’ila ce ke kai hare-harenta kan Gaza, kuma zuwa 2025 kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya ya ayyana shi a matsayin kisan ƙare-dangi a hukumance.

An kashe fiye da Falasdinawa 67,000 waɗanda akasarinsu mata da yara ne, kana kusan 170,000 sun jikkata, sannan an jefa ɗaukacin al’ummar yankin cikin yunwa da yin ƙaurar dole.

Yanayin ya jefa Gaza cikin yunwa, ba wai haka siddan ba, amma ta hanyar da aka tsara da gangan.

'Yunwa a matsayin makamin kisan ƙare-dangi'

Tsarin Isra’ila na hana abinci da ruwa da kuma man fetur ya haifar da ɗaya daga cikin mafi munin matsalar jin-ƙai da aka taɓa gani a ƙarni na 21.

A ƙarshen watan Agusta, Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar a hukumance cewa akwai yunwa a Gaza, lamarin da ya tabbatar da abin da wasu ƙungiyoyin agaji da na kare haƙƙin bil-adama suka daɗe suna faɗa tsawon watanni.

Ga Ramy Abdu, shugaban ƙungiyar da ke sa-ido da kuma kare haƙƙin bil-adama ta Euro-Med mai hedkwata a Geneva, katange Gaza da Isra'ila ta yi na daidai da "manufar amfani da abinci da ruwa a matsayin makamin yaƙi da na kisan ƙare-dangi".

‘‘Yunwar Gaza ta sha banban da na sauran, domin ba wai bala’i ne haka siddan ba, ko kuma na taɓarɓarewar tattalin arziƙi ba," a cewar Abdu.

Ya ƙara da cewa, ‘‘Da gangan ake amfani da yunwa wajen kashe fararen hula."

Tun shekara ta 2006 Isra’ila ke ci gaba da iko da kan iyakokin Gaza, inda har ma a wasu lokuta take lissafa adadin kuzarin da aka yardar wa kowane Bafalasɗine ya ci a rana.

Lokacin da ta ayyana ‘‘cikakkiyar mamaya’’ a ranar 9 ga watan Oktoban 2023 - gabakiɗaya Isara’ila ta yanke shigar da abinci da ruwa da mai da kuma wutar lantarki, nan take tsarin abinci ya rushe a yankin mai rauni.

Masu AlakaTRT Afrika - Shekaru biyu na kisan kiyashi: Yadda Isra'ila ta jefa Gaza cikin yunwa

Da rufewar gidajen biredi, da katsewar ruwan famfuna da kuma gonaki da aka yi musu ruwan bama-bamai, yunwa ta zama makami. An haramta kamun kifi tare da lalata hanyoyin noma na Gaza. Babu wata hanya a yankin da ta rage wa Falasɗinawa.

Mamayar Isra’ila ta mayar da raunin da ta haifar cikin shekaru zuwa makamin hallaka yankin sannu a hankali,’’ in ji Abdu.

Yunwa ta yi ta yaɗuwa cikin sauri a farkon wannan shekarar. Yara da mata masu juna-biyu da kuma tsoffafi ne suka yi ta mutuwa.

An tare ayarin motocin agaji, kuma a lokacin da fararen-hula suka yi ƙoƙarin isa yankin da "Gaza Humanitarian Foundation" wanda Isra'ila ta kafa a shekarar 2025, sun gamu da munanan hare-hare.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an kashe Falasɗinawa fiye da 1,760 a ƙoƙarinsu na samun kayan abinci, kusan 1,000 daga cikinsu a kusa da wuraren da aka ware.

"Wannan ba ƙaramin irin tashin hankali ba ne," in ji Abdu. "Manufar yunwa ce da aka tsara ta cikin hikima."

An ayyana yunwa, an jinkirta ɗaukar mataki

A ranar 22 ga watan Agustan 2025, shirin tabbatar da tsaron abinci na Majalisar Dinkin Duniya (IPC) ya ayyana "yunwa" a Gaza bayan yin duba kan dukkan matakai uku masu muhimmaci da ake keta - tsananin ƙarancin abinci, da rashin abinci mai gina jiki da kuma mace-mace masu nasaba da yunwa.

Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu a Gaza ta ba da rahoton mutuwar aƙalla mutane 460 sakamakon yunwa, ciki har da yara 150, yayin da yaro ɗaya cikin yara biyar a birnin Gaza yake fama da tamowa.

Amma duk da haka ko bayan ayyana yunwa da Isra'ila ta tilasta, babu wani martani mai ƙarfi daga ƙasashen duniya.

‘‘Duniya ta kasa tilasta wa Isra’ila wadda ke ci gaba da yin watsi da ƙudurorin MDD, inda take samun goyon bayan Amurka da Turai," in ji Abdu.

Bayan wata ɗaya, a hukumance kwamitin bincike na MDD mai zaman kansa ya gama tattara bayanansa kan cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi, inda ta cika ayyuka huɗu cikin biyar da aka ayyana ƙarƙashin yarjejeniyar kisan ƙare-dangi ta 1948: kisan jama’a, cutar da jiki da ƙwaƙwalwa, da kuma lalata yanayin rayuwa da hana haihuwa.

‘‘Ayyana ayyukan Isra’ila a matsayin kisan kiyashi ya kamata ya haifar da wajibcin dakatarwa da kuma hukunta ta,’’ in ji Abdu,. ‘‘Amma a aikace, ba a yi ko kaɗan ba.’’

'Yaƙi mafi muni ga 'yan jarida'

Duk da cewa yunwar da Isra’ila ta tilasta da kuma ruwan bama-bamai da suka lalata Gaza, ‘yan jarida Falasɗinawa sun ci gaba da bayar da rahotanni.

Daga cikinsu har da wani ɗan jarida mai zaman-kansa na TRT World, Yahya Barzaq wanda aka kashe a wani hari da Isra’ila ta kai a ranar 30 ga Satumban 2025, yayin da yake ƙoƙarin ɗaukar hotuna a Deir al Balah.

Kafin yaƙin, an san Barzaq a matsayin mai ɗaukar hoton jarirai, shafinsa na sada zumunta cike yake da hotunan jarirai. Bayan watan Oktoba na 2023, shafukan sun koma na baraguzai da tarkace, da kuma jana'iza da baƙin launi na baƙin ciki.

"Na tsinci gangar Jikina a kudu, amma zuciyata har yanzu tana birnin Gaza," kamar yadda ya rubuta a saƙonsa na ƙarshe.

Barzaq ya zama ɗaya daga cikin ‘yan jarida da ma’aikatar yaɗa labarai aƙalla 250 da aka kashe tun lokacin da aka fara yaƙin, wanda ya sa Gaza ta zama wuri mafi muni ga manema labarai a tarihin wannan zamanin.

Kafofin yaɗa labaran Falasɗinawan sun ce wadannan mace-mace ba na ganganci ba ne, amma wani gangami ne na koƙarin rufe bakin masu ba da labarin Gaza ne.

Duk da haɗarin da ke tattare da hakan, 'yan jarida na ci gaba da tattara bayanan ta'addanci, ƙyamarorinsu na ɗaukar yanayin yunwa da wahala da ake ɓoye wa duniya.

Haifar da matsalar tattalin arziƙi

Mumunan tashin hankalin da ke faruwa a Gaza ya kuma haifar da matsalar tattalin arziƙi ga duniya.

An samu gagarumin ƙauracewa manyan kamfanonin ƙasashen duniya da ake zargi da tallafawa ko ciyar da ayyukan Isra’ila gaba.

Manyan kamfanoni irin su McDonald's, da Starbucks, da Coca-Cola, da Nestle da Nike sun fuskanci faɗuwar ciniki tare da ɓacin suna a kasuwannin ƙasashen da musulmai suka fi yawa.

Alal misali, McDonald ya ba da rahoton faɗuwa a cinikinsa a rubu’in farko na shakara a cikin shekaru huɗu.

Kazalika Starbucks ya fuskanci raguwar kashi 36 cikin 100 na kasuwancinsa a Malaysia da kuma asarar kashi ɗaya cikin huɗu a duniya.

Ƙuɗaɗen da kamfanin Nike ke samu a duniya ya ragu da kashi 12 cikin ɗari a rubu'i na biyu na shekarar 2025, yayin da ribar da ya samu ta ragu da kashi 86 cikin ɗari, kana ƙauracewa kamfanin ta ƙara tsananta.

Cinikin kayan shaye-shaye shi ma ya fuskanci koma-baya. Kasuwar Coca-Cola a Turkiyya ta ragu daga kashi 59 zuwa kashi 54, haka kuma ribar da Nestle ke samu ta ragu da sama da kashi 10 cikin ɗari a farkon shekarar 2025.

Kazalika masu zuba jari sun lura da hakan.

Ƙasar Norway ta karkatar da dala triliyan 2 na asusu na musamman na ƙasar daga bankunan Isra’ila biyar da kamfanin kayayyakin haƙo ma’adinai na Amurka saboda "hadarin da ba za a amince da shi ba" na ba da gudummawa ga laifukan yaƙi.

Babban asusun fansho na Netherlands ya bi sahu, inda ya sayar da dukkan hannun jarinsa na kamfanin kayayyakin haƙo ma’adinan wanda ya kai Euro miliyan 387, bisa alaƙar kamfanin da sojojin Isra'ila.

Laifukan rashin sanin yakamata Turai

Babu wani yanki da mutuncinsa ya ɓaci kamar na Tarayyar Turai.

Lokacin da aka fara yaƙin Isra'ila, shugabannin Tarayyar Turai Ursula von der Leyen da Roberta Metsola sun yi saurin zuwa Tel Aviv don nuna goyon bayansu.

Bayan shekaru biyu, wannan goyon baya ya ragu zuwa nadama da rabuwar-kai.

Sakamakon matsin lamba daga duniya, Brussels ta yi nazari kan yarjejeniyar haɗin gwiwarta da Isra'ila, tana mai nuni kan "cin zarafin bil'adama".

Hukumar Tarayyar Turai ta ba da shawarar dakatar da ribar kasuwanci, da sanya takunkumi ga masu tsattsauran ra'ayi na Isra'ila, da kuma dakatar da asusunsu - amma aiwatar da hakan bai yiwu ba saboda rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobin ƙungiyar.

Yayin da Sifaniya da Ireland suka yunƙura don ɗaukar mataki, wasu, musamman Jamus, sun nuna adawa, suna takatsantsan karya alaƙa da Amurka da Isra'ila.

Masu suka sun ce wannan shakku ya mayar da ƙungiyar EU daga jagora mai sanin yamata zuwa yar kallo.

Kenneth Roth, tsohon jami'in kare haƙƙin bil'adama na ƙungiyar Human Rights Watch, ya ce EU "ta kasa gane tun da wuri cewa yaƙin Isra'ila ya rikiɗe zuwa yaƙi a kan fararen-hula na Gaza".

“Yawancin ƙasashen Turai sun daina sayar wa Isra’ila da makamai, wasu kuma sun amince da Falasɗinu a matsayin ‘yantanciyar ƙasa, sai dai har yanzu ƙungiyar ba ta yi tsayin-daka kan Amurka ba," in ji shi.

Tambayar ita ce ko EU za ta matsa wa Washington lamba kan ta daina ruruta wutar kisan kiyashi."

Claudio Francavilla na ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch ya bayyana martanin EU da "wanda ya makara".

"Bisa tsarin doka, Turai tana da ikon hana kisan kiyashi a ƙarƙashin yarjejeniyar 1948, amma ba a yi hakan ba," in ji shi. "E, akwai cigaba - takunkumi, da sauye-sauyen siyasa - amma gaskiyar ita ce Isra'ila na rasa abokantaka a Turai saboda rashin tausayi."

Ga Niamh Ni Bhriain ta Cibiyar Tattalin Arziƙi ta Ƙasashen waje, gazawar EU ta kasance darasi babban kan sanin yakamata.

"A duniyar da ake yin adalci, shugabannin EU za su fuskanci shari'a a birnin Hague bisa laifin hannu wajen kisan ƙare-dangi, amincinsu ya tabarbare," in ji ta.