| hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Kisan ƙare-dangi: Isra'ila ta kashe yara 20,000 a Gaza ta hanyar amfani da tan 200,000 na bama-bamai
Kusan Falasɗinawa miliyan biyu ne aka tilastawa gudun hijira tun farkon yaƙin Isra'ila a Gaza.
Kisan ƙare-dangi: Isra'ila ta kashe yara 20,000 a Gaza ta hanyar amfani da tan 200,000 na bama-bamai
kusan Falasdinawa miliyan biyu ne aka tilastawa gudun hijira tun farko yakin Istra'ila a Gaza
6 Oktoba 2025

Isra’ila ta kashe yara kusan 20,000 a yayin kisan ƙare-dangi da take yi a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana a ranar Lahadi.

Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza ya ce an kai gawarwakin yara fiye da 19,450 asibitoci, yayin da kuma aka kashe mata fiye da 12,500, ciki har da 10,160 waɗanda aka gano gawarwakinsu.

Ofishin ya ce sojojin Isra'ila sun lalata kusan kashi 90 na yankin Gaza tare da mamaye fiye da kashi 80 cikin 100 na yankin, ta hanyar amfani da bama-bamai da aka ƙiyasta kimanin tan 200,000.

A cewar sanarwar, an kashe aƙalla jami’an kiwon lafiya 1,670, da jami’an tsaron farar-hula 140, da kuma ‘yan jarida 255 tun bayan fara yaƙin shekaru biyu da suka wuce.

Ofishin yaɗa labaran ya ce, kimanin mata masu juna biyu 12,000 ne aka samu rahoto zubewar cikinsu a Gaza saboda yunwa da kuma lalata tsarin kiwon lafiya da Isra’ila ke yi.

Kazalika rahoton ya zargi Isra’ila da amfani da ‘dabaru na musamman‘ wajen kai hari kan sashen kiwon lafiya na Gaza tare da lalata asibitoci 38, da cibiyoyin kiwon lafiya 96, da motocin ɗaukar marasa lafiya 197.

Ofishin ya ce an rusa masallatai 835 sannan 180 sun lalace, yayin da aka kai hari kan majami'u uku, kana an lalata maƙabartu 40, an kuma sace gawarwaki fiye da 2,450 a wuraren da aka binne su.

Masu AlakaTRT Afrika - Isra'ila ta rusa duka unguwar Al Zeitoun mai gidaje fiye da 1,500 a Birnin Gaza

Haka kuma rahoton ya ce, an ruguza rukunin gidaje 268,000 , yayin da 148,000 suka lalace sosai, sai kuma 153,000 da suka ɓaci, kazalika an raba iyalai fiye 288,000 daga matsugunansu.

Yawancin tantuna 125,000 da ke ba su mafaka, a yanzu ba su da kyau da za a iya ci gaba da zama.

Kusan Falasɗinawa miliyan biyu ne aka tilastawa gudun hijira tun farkon yaƙin Isra'ila a Gaza, kana hare-haren Isra’ila sun lalata matsugunai da cibiyoyin mafaka 293, in ji rahoton ofishin.

Rumbun Labarai
Bayanai na hukuma sun nuna cewa sojojin Isra'ila sun yi yunkurin kashe kansu sau 279 cikin wata 18
Hare-haren Isra'ila a Gaza sun kashe mutane 91, ciki har da yara 24, duk da tsagaita wuta
Netanyahu ya ba da umarnin a kai 'hare-hare masu karfi' kan Gaza
Shin Trump zai yanke alaka da Isra'ila idan ta ci gaba da mamaye Gabar Yammacin Kogin Jordan?
Amurka ta tsare ɗan jaridar Birtaniya Musulmi mai suna Sami Hamdi saboda sukar Isra'ila
Fiye da tan miliyan 61 na tarkace da baraguzai sun rufe Gaza a shekara biyu na yakin Isra'ila: UNRWA
Kalaman Trump na lalata cibiyoyin nukiliyar Iran 'mafarki ne': Khamenei
Wata ƙungiyar bayar da agaji ta Turkiyya ta ƙaddamar aikin kwashe ɓaraguzai a arewacin Gaza
Sojojin Israila sun buɗe wuta kan wasu manoma Falasɗinawa a yayin da suke girbe zaitun a Gaɓar Yamma
Mene ne abu na gaba a shirin zaman lafiya na Gaza?
Isra'ila ta sake buɗe mashigar Rafah don bai wa manyan motocin kayan agaji damar shiga Gaza
Turkiyya, Masar, Qatar da Amurka sun sa hannu kan takardar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Dauwamammen zaman lafiya zai samu ne kawai ta hanyar kafa ƙasashe biyu, Erdogan ya faɗa wa Starmer
Sojojin Hamas sun kashe mutum 32 cikin 'gungun' da ke sace kayan agaji a Gaza
Hamas ta kammala sakin 'yan Isra'ila 20 da ta tsare a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta
Wani bidiyo ya nuna yadda Isra'ila ke cin zarafin fursunonin Falasɗinawa gabanin sakin su
Trump, Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza a birnin Sharm el-Sheikh a ranar Litinin
Sojojin Amurka sun isa Isra'ila domin sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Sojojin Isra'ila sun fara janyewa a hankali zuwa gabashin Gaza: Kafofin watsa labarai
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta Trump