Kisan ƙare-dangin da Isra’ila ke yi a Gaza da ta yi wa ƙawanya ya shiga shekara ta uku.
Bayan kwanaki 732 na zubar da jini, Isra’ila ta kashe sama da Falasɗinawa 67,000, wani ƙiyasin mai sauƙi wanda masana ke ganin ya yi ƙasa sosai da adadin waɗanda lamarin ya shafa.
Tsawon lokacin da aka yi kisan ƙare-dangin, Isra’ila ta lalata yawancin yankin kuma ta raba dukka mutanen da muhallansu.
Gwamnatin Tel Aviv ta lalata komai, daga makarantu da asibitoci da masallatai da coci-coci da ma tantunan ‘yan gudun hijira.
Kisan ƙare dangin ya zama yaƙi mafi muni ga ‘yan jarida a tarihin wannan zamanin, bayan Isra’ila ta kashe kusan ‘yan jarida 250 da ke aiki wa kafafen watsa labarai.
Ƙiyasin Majasalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya nuna cewa Isra’ila ta kashe sama da mata da yara 28,000 a Gaza. Ma’aikatar Lafiya ta Gaza kuwa ta ce Isra’ila ta kashe sama da yara 20,000.
Isra’ila ba ta ƙyale masu aikin jinƙai ba, kuma MDD ta ce ta kashe aƙalla 383 daga cikinsu.
A hanlin yanzu ana tattaunawar sulhu a birnin Alƙahira na Masar, amma wannan bai hana Isra’ila ci gaba da kai hare-hare da kuma kashe Falasɗinawa a Gaza ba.
Ga kaɗan daga cikin wasu hotuna da suka yi ƙaurin suna daga kisan ƙare-dangin da aka shafe shekara biyu ana yi:
Isra’ila ta kama farar-hular Falasɗinawa, ta rufe musu idanu ta tuɓe musu tufafi.
Gawarwakin Falasɗinawa da Isra’ila ta kashe an tara su a wani asibiti a farko-farkon kisan ƙare-dangin.
Sojojin Isra’ila sun sace ‘yar-tsana daga yaran Falasɗinawa
Isra’ila ta kashe kusan ‘yan-jarida 250 a Gaza.
An yunwatar da ɗaruruwan yara har suka mutu saboda hana shiga da kayan agaji da Isra’ila ta yi.
Ƙungiyar Yahudawa ta Neturei Karta Jews ta shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Washington DC. / Hoto: TRT World Archive
Ma’aikatan agaji na Red Crescent da Isra’ila ta kashe. / Hoto: AP Archive
Falasɗinawa da aka mamaye suna rububin karɓar abincin jin-ƙai.
Falasɗinawa da aka tilastawa ƙauracewa yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai musu hari.
Isra’ila ta kashe aƙalla mata da yara 28,000 a Gaza.
Ɗalibai a Amurka suna zanga-zangar kisan ƙare-dangin Isra’ila a Gaza suna fuskantar tsangwama daga hukumomin Amurka.