Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta fitar da wani cikakken shiri mai dauke da gabobi 20 da nufin kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma samar da zaman lafiya na tsawon lokaci, a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Kudirin neaman zaman lafiyar da aka fitar a ranar Litinin ya yi hasashen mayar da Gaza zuwa "yankin da ba shi da ta'addanci wanda ba ya haifar da barazana ga makwabtansa" tare da tabbatar da cewa "za a sake gina shi don amfanin al'ummar Gaza, wadanda suka sha wahala fiye da yadda ake iya tunani."
A karkashin shirin, "idan bangarorin biyu suka amince da wannan shawara, nan take yakin zai kawo karshe" tare da janye sojojin Isra'ila zuwa wuraren da aka amince su zauna.
A cikin sa'o'i 72 da amincewar Isra'ila, dole ne a dawo da duk wadanda aka yi garkuwa da su, na raye da wadanda suka mutu, kamar yadda tsarin shirin ya nuna, wanda kuma aka watsa a shafukan sada zumunta.
Bayan sakin fursunonin da aka yi garkuwa da su, Isra'ila za ta saki fursunoni 250 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai da kuma mutanen Gaza 1,700 da aka tsare bayan 7 ga Oktoban 2023.
Mambobin Hamas da suka "yi alkawarin zaman lafiya tare da ajje makamansu za a yi musu afuwa."
"Bayan amince wa da wannan yarjejeniya, nan take za a aika da cikakken taimako zuwa zirin Gaza," tare da rarraba wa "ba tare da tsangwama daga bangarorin biyu ta hanyar Majalisar Dinkin Duniya da hukumominta ba."
Gudanarwa, sake gina Gaza
A cewar shirin, Gaza za ta kasance karkashin "kwmitin Falasdinawa kwararru da ba ruwan su da siyasa" wanda ke da alhakin ayyukan yau da kullum.
Hamas da sauran bangarorin ba za su kasance "ba su da wani matsayi a mulkin Gaza, kai tsaye, ta hanyar amfani da wasu, ko ma ta kowace fuska."
Amurka za ta yi aiki tare da kawayenta Larabawa don aika wa da Rundunar Tsaro ta Duniya ta wucin gadi (ISF).
Idan Hamas ta ki amincewa da shawarar, "aikin taimakon da aka tanada" zai ci gaba a yankunan a karkashin kulawar ISF.
A tanade-tanaden shirin, abokan hadin gwiwa na yankin za su "tabbatar da cewa Hamas, da bangarorin, sun sauke nauyin da ke wuyayensu, kuma sabuwar Gaza ba ta da wata barazana ga makwabtanta ko al'ummarta."
"Isra'ila ba za ta mamaye ko kuma cinye Gaza ba," tare da janye sojojinta a yayin da dakarun kasa da kasa ke kafa iko a yankin.
Shirin bunkasa tattalin arzikin Trump na "sake gina wa da karfafa wa" Gaza kuma zai kafa "yankin tattalin arziki na musamman tare da bayar da fifikon kudin fito da kudaden shiga" da aka yi yarjejeniya da kasashen da abin ya shafa.
“Babu wanda za a tilastawa barin Gaza, kuma wadanda ke son fice wa za su samu ‘yancin yin hakan kuma su dawo,” in ji sanarwar.
Shirin ya hada da tsarin tattaunawa kuma ya bayyana cewa "lokacin da aka aiwatar da shirin gyare-gyare na Hukumar Falasdinu (PA) cikin aminci, a karshe za a iya samar da yanayi mai inganci don tabbatar da 'yancin kai da kafa kasar Falasdinu."
Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 66,000, yawancin su mata da yara a Gaza tun daga watan Oktoban shekarar 2023.
Hare-haren bama-bamai da aka kai ba tare da kakkauta wa ba sun saka yankin ya zama mara matsuguni kuma ya haifar da yunwar da dan adam ya janyo.